بِسْمِ اَللهِ اَلرَّحْمَنِ اَلرَّحِيمِ
Gabatarwa:
Dasunan Allah
maiyawan rahama maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga
fiyayyan halittar Allah, manzan tsira Annabi Muhammad da Iyalan Sa da Sahabban
Sa baki daya da wadanda suka bi bayansu da kyautatawa izuwa ranar sakamako,
amin.
Bayan haka, hakika wannan bita da 'yan uwa suka
shirya a Shirin Hasken-Musulunci anan Minna, fadar Jahar Neja ayau (Alhamis: 4,
ga Ramadan 1432 daidai da 4, Agusta 2011) lallai tana da matukar muhimmanci
musamman a irin wannan lokaci, wanda yake a fili take irin gudun mawar da
ladanai suke bayarwa a cikin al'umma baki daya.
Wannan
matashiya da zamu tattauna a kanta maitaken "Kura-Kuran da ake samu a kiran
sallah'' muna fatan ta zama wani abune da za mu yiwa juna gyara, don gyara
kayanka bai zama sauke mu raba ba, kuma muna so a wannan haduwa ya zana an
magance wadannan kura-kurai duddacewa ba su ke nanba, amma har idan muka gane
cewa akwai kurakuran kuma muka dauki hanyoyin gyara to zamu sami taimakon Allah
akai, Allah ya yi mana jagora amin.
A
cikin wadannan kurakurai akwai wadanda su ke da alaka da maikiran sallah, akwai
kuma wadanda suke da alaka da ma'anonin kiran sallah ta yadda idan ma'anar ta
canza sai ta maida shi ba kuma kiran sallah ba. Sannan akwai wadanda suke da
alaka da al'umma baki daya, lalle wanan yana nuna mana cewa matsayin ladaini a
cikin al'umma ba karamin matsayi bane, muna rokon Allah da sunayan kyawawa da
siffofin sa madaukaka ya yima jagora amin.
A
yanzu za'a dan lissafa wasu daga ciki, ayi kuma dan karin haske sannan abada
shawarwari.
Akwai wadansu
abubuwa da zasu shiga cikin kura kuran da ake samu a kiran sallah, kamar:
1. Rashin Kiran
Sallah A Farkon Lokacinta: Kamar yadda malamai suka zayyana bayana a littafai
cewar kiran sallah shi ne: Sanar da mutane shigar lokacin sallah. Kuma
kamar aka sani kowacce sallah tanada lokacinta kuma gashi malam ya kara mana
bayi ya kuma fito mana da lokatan fili, wanda rashin kiran sallah a farkon
lokacin ta ya haifar da angama kiran sallah sai a tada ikama, wanda anasone
tsakanin kiran sallah da tada ikama a sami tazara ta yadda mara alwala zai yi
alwala, wanda sai ya yi tsarki ya je ya yi tsarki, anan kenan zamu gane yana
daga cikin manyan ayyukan ladan da lokacin sallah ya yi ya kita domin ya sanar
da al'umma shigar lokacinta.
Babbancin
kiran sallah da ikama shine: Kiran sallah sanar da mutane shigar lokacin sallah
(Ladani kuma shi ya kamata ya fi kowa tantance lokutan sallah), ita kuma ikama:
sanar da wadanda ke cikin masallaci anfara sallah.
2. Rashin Tantance
Lokaci: Ladani ya sani shi ne mutum na farko da yafi kowa sanin canjin lokaci
da yadda yake karuwa da kuma yadda yake raguwa, kuma idan zai yi anfani da
agogo kada ya dogara da agogo daya, ya zamana yana dasu uku ko hudu, rashin
wannan wadansu ladanan suke kiran sallah tsakaddare ko dab da magariba idan
hadari ya rufe rana.
Ladanifa
ya sani sallolin mutane da azuminsu suna ratayene a wuyanshi, miliyoyin mutane basa shanruwa ko
su dakatar da sahur sai ladan ya kira sallah.
3. Rashin Tsayawa A
Koyi Kiran Sallah: wannan yana daga cikin manyan matsalolin da ake samu, ta
yadda inda za'a kowa ya fadi malamin da ya koya masa kiran sallah to da anyi
zuffa. Hakan ya haifar da kowa yake yin yadda ya ga dama, wasuma ka ji da
yarukansu suke yi ba da larabciba.
4. Rashin Tantacce
Ladanai A Masallaci: wannan yasa kowa ya zama ladani, wanda yake wannan kuwa
kuskure ne, wannan baihana a sami ladanai a masallaci gudaba, su zama biyu ko
uku ko dai gwargwadon abida ya sawwaka amma tsayyayu, wannan zai sa asan cewa ladani
wane yana kiran sallar asubahine kafin alfijiri ya keto amma ladani wane sai
bayan alfijiri, kamar yadda ya kasance tsakanin Bilal da Ibnu ummi maktum Allah
ya kara musu yarda.
5. Rashin Sanin
Ma'anonin Kiran Sallah: wannan ya haifar da abubuwa masu yawa, da basa cikin
addini, misali: Ladani ya kammala kiran sallah sai yace 'Ayi alwala, a
jaddada' inda yasan ma'anar
حَيَّ عَلَى اَلصَّلاَةِ، حَيَّ عَلَى
اَلْفَلاَحِ
Hayya alas Swalah,
Hayya alal Falah da bai fadi waccar maganarba.
6.
Rashin Kula Da Ladubban Sallah: wannan ya sa sai kaka ladani yana kiran sallah
amma sai kaga kamar yana wani abu da bashi da alaka da addini, wani lokacin sai
ya yi kamar ya juyawa alkibla baya.
7. Kura kurai a
lafuzza: ana samun kurakurai masu tarin yawa a lafuzzan kiran sallah. Wadannan
kurakurai sun kashi kashi biyu.
(a) Kuskure mai
canza ma'ana: irin wadannan kura-kurai suna fitar da shi daga kiran
sallah kwatakwata ya zama wani abu daban, misali:
اَللهُ أَكْبَرُ – أَكْبَارُ
(b) Kuskure na bata lafuzza: wanda yake fitar da shi daga duniyar larabci, misali:
أشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رسولُ اللهِ
Shawarwari:
A takaitaccen wanna jawabi da kuma
wadannan abubuwa dana gani ina bada shwara kamar haka:
1. Bayar da mintina
bayan kiran sallah kafin tayar da sallah, wannan ko zai tabbatane idan ankira
kowacce sallah a farkon lokacin. Misali Azahar minti 20 la'asar minti 15
magariba minti 10 lisha minti 15 asuba minti 20.
2. Ladani ya zama
yana da agogo kamar uku banda na wayarshi, kuma ba zaije kiran sallah ba sai ya
duba su duka.
3. Aiki da dukkan
abubuwan da aka gabatar a wannan bita.
4. Gyara inda duk
mutum ya ji yana da kuskure.
5. Isar da wadannan
bayanai ga wadanda basu zo wannan bita ba.
6. Ladanai su samara
da wata haduwa da zasu dinga yi lokaci lokaci domin tuntubar juna koda ko za'a
fara a matakin unguwa unguwa ne.
7. Ci gaba da shirya
irin wannan bitar lokaci bayan lokaci
8. Koyon kiran
sallah baki da baki daga wurin malamai masana.
Allah ya gafartamana ya kuma ya fe
mana, Allah ya karbi ayyukammu amin summa amin.
وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu,
bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar
Neja Nijeriya.
Za'a iya
tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu
Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad Sadisu
No comments:
Post a Comment