Matashiya: Hakika Allah mai
girma da daukaka ya shar'anta tsarkaka daga hadasin da yake karami ko babba
kafin gabatar da sallah, wannan tsarkaka kuma bata yiwa sai da ruwa mai tsarki
mai tsarkakewa, gabatar da wannan tsarki da kuma rowan da aka ambata shine
abinda yake wajibi muddin akwai dama, sai dai akan sami wasu lokuta da ake rasa
rowan kwatakwata ko kuma ga ruwan amma idan aka yi alwala da shi ko wanka za'a
rasa wanda za'a sha, koma yin anfani da rowan zai haifar da wasu cututtuka da
dai sauran wasu dalilai shar'antattu da zasu hana amfani da ruwan to akan haka
aka shar'anta Taimama domin sawwakewa al'umma, da kuma dauke dukkan wata damuwa
akan hakan.
Mecece Taimama?: Taimama itace;
Shafar fuska da hannaye a wuri mai tsarki ta yana yi kebantacce.
Kenan ba kowacce shafar fuska da hannu ne
yake zama taimama ba, sannan kuma ba a kowanne wuri ake yi ba, sannan ba yadda
aka ga dama ake yi ba.
Tabbatuwar Taimama: Taimama ta tabbata
daga haske na Alkur'ani da kuma Hadisan ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allan
su tabbata a gareshi- kana da ijima'in malamai.
Tabbatuwarta A
Kur'ani: Allah ya yi bayanini shar'antuwar taimama a cikin Alkur'ani mai girma
a Suratun Nisa'I, aya ta 43, da kuma Suratul Ma'idah aya ta: 6. amma ayanzu
zamu kawo bayani akan ayar suratul ma'idah, wato aya ta shida kenan, Allah
madaukakin sarki yana cewa:
''Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani!
Idan kun tashi za ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da kuma hannayanku zuwa
gwiwar hannu, ku kuma shafi kawunanku
kuma ku (wanke) kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun kasance masu janaba
to ku tsarkaka (ku yi wanka), idan kuma kun kasance marasa lafiya ko kuna kan
tafiya ko kuma daya daga cikinku ya yi bayan gida, ko kuma kun taba mata
(janaba) baku sami ruwa ba to sai ku yi taimama a wuri mai tsarki sai ku sahfi
fuskokinku da kuma hannayanku daga wurin, Allah baya nufin ya sanya mukun kunci
ko kaka, saidai yanason ya tsarkake ku kuma domin ya cika ni'imarsa a gareku
domin ku gode masa. (Ma'idah, aya ta:6).
Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi
hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake karyata, da kuma janaba da yadda ake
wankan tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi taimamar da kuma yadda ake
yenta, sannan da manufar da tasa Allah ya shar'anta taimamar, Allah muna gode
maka, akan wannan ni'ima.
Tabbatuwar Taimama
A Hadisi: Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi-
yace: ''An bani abubuwa biyar da ba'a ba wani ba kafin ni; An taimakamin
da tsoro (ma'ana sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira tsawan wata guda,
kuma an sanya min kasa ta zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani mutum
daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to ya yi sallar shi'' a wata
riwayar ''To anan inda yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''.
Bukhari, Hadisi na: 335, Muslim Hadisi na: 521.
Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin
ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan al'ummar gatan da bai yiwa wata
al'ummaba, a ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta zama wurin sallah,
al'ummomi da suka gabata basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu, amma mu
ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace
an sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi tsarki da ita kamar yadda
bayanai suka gabata a baya akan istijmari, sannan kuma zaka yi taimama da ita
kamar yadda ake kawo bayani a yanzu haka.
Taimama matsayine na musamman da wannan
al'umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya taimama ga wata al'ummaba kafin
wannan al'ummar domin yalwatawa ga wannan al'ummar.
Ijima'i:
Malamai duk sun yi ijima'i akan tabbatuwar taimama.
Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a
shar'ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan abinda kasan ba'a yi said a ruwa
to ana yi da taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur'ani da dai sauransu.
Taimama Tana Tsayawa Matsayin A Lokuta Kamar:
Kenan anan za'a lissafo abubuwan da suke sawa a yi taimama, domin kada kabar
sallah ta wuce maka kace ai baka sami ruwa bane wannan ba zai sa ka sami
sassauci ba domin sabo da hakan aka shar'anta taimama, wadannan wurare sune
kamar haka:
1. Rashin Ruwa: Kasan cewa suna
cikin tafiya ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun nema iya yadda za su
iya basu sami ruwan ba, to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su bari
lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai su gabatar da taimama su yi sallar
su, ko da a cikin su akwai masu janaba, ko matan da al'adar su ta dauke. Kuma
da zarar sun gabatar da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko da an sami
ruwa ba za su sakeba. Wato shi addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane shi a
yadda yake gwargwadon yadda yake da sauki a gareka.
2. Ruwan Ba Zai
Isaba: Idan kuma a tare da ku akwai ruwan amma kuna da matukar mukata domin
shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi za ku ba dabbobi ko shi kuke sawa a
injin mota ta yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe ku wadancan
bukatuba, asalima za'a iya tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa to amma
miyagun namun dajine a wurin ko kuma matattarar barayine wurin to anan fa
hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa, saboda haka wadanda suke dashi kadan
domin bukatunsu sai su sha su yi taimama.
3. Cuta: Idan ga ruwan,
amma ka ji tsoron cuta a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin warkewa, sai
ka yi taimama.
4. Rashin Motsi: Idan ya zamana
yana fama da rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai iya motsawaba
domin ya debo ruwan alwalar kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko babu
wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya yi taimama.
5. Sanyi: Idan yana matukar
jin tsoron sanyi idan ya yi anfani da ruwa, kuma ga shi yana son yin alwala ko
wankan tsarki ga shi bai sami abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya yi
taimama.
Wadannan bayanan suna nuna mana cewa rashin
lafiya bata dauke sallah, domin koda ba zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko
jinkirin warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da aka ambata to sai ya yi taimama,
abin takaici shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya to abu na farko da
zai ajiye shine sallah, inda zaka je gai dashi kace ya yi sallah kuwa sai ka ga
ana kallonka ana nuna maka halin da yake ciki kamar kai baka da tausayi, inda
kuma zaka dan shafa masa dari ko dari biyu sai ya miko hannu, Allah Ya sawwake.
Hakanan inda mutum za'a tsare shi, ba zai
bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba'a barinsu su yi alwala to ba sai ya
yi taimamaba.
Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa
kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa akan bandejin ko karan dorin to sai
ya yi alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba sai ya wankeba.
Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya
zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan kai tsaye sai ya wuce zuwa
taimama. Shi bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi sannan ayi shafa
akan wasu gabobi sabo matsanancin rashin lafiya day a shafi gabban alwala ko
taimama darasine mai zaman kansa, a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma
sha-daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin cututtuka da zasu sami gabban
alwala, kuma ya kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan taimama a fasali na
goma, Allah ya saka masa da alkhairi.
Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake
doron kasa kamar inda yake; rairayi ko jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar
gishiri ko ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace.
Siffar Taimama: Yadda ake gabatar
da taimama shine; zaka wara yatsun hannayanka biyu ne sai ka buga a kasa,
sannan sai ya shafi fuskassa da cikin tafikan hannunsa, sai kuma ya shafi
hannayansa zuwa wuyan hannu (Ku'i), zai yi ko kari ya tabbata ya game ko'ina na
fuskarsa a lokacin da yake shafar kar ya manta da karkashin gemu da kuma
hannayansa, idan yana da zobe sai ya cire domin shafar ta game ko ina, idan
lokacin da ya shafo kasar kwai yayi ko kura sai ya karkade, ba'ace dole sai
mutum ya sa kasa a fuskarsa ba.
Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau
biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun kuma ya shafi hannuwa zuwa
gwiwar hannu.
Za'a ko yi yadda ake taimamane da sauran
ibadu a gaban malamai, karantawa anan kadai ba zata wadatarba, su kuma malamai
su ji tsoron Allah su koyawa al'umma wadannan ayyuka a'aikace, sawa'un makarantun
islamiyyune ko malaman da suke koyar da darussan addinin musulunci a cikin
jami'o'i ko a kwalejojin ilimi, ko kuma malamai da suke karantarwa a cikin
masallatai, kada ka taba jin dan ka karantar da baki kowa ya gane, a'a sai ka
yi a aikace, kada ka manta sai da ma'aikin Allah ya koyawa sahabbansa wadannan
ayyuka a aikace, ka ko san idan saurin ganewane sun fika sun fi daliban da kake
koyarwa.
Abundake Bata Taimama; Taimama tana
baci da duk abinda yake bata alwala babbane ko karami, kamar tusa fitsari….
Fitar maniyyi, jinin al'ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi taimama ya
gushe to taimama ta gushe.
Wanda ya rasa ruwa kuma ya rasa kasar da zai
yi taimama akanta, ko kuma ya kai wani halin dab a zai iya taba ruwaba ko kasa
to shi wannan zai yi sallar ne a yadda ya sami kansa, ba tare da alwala ko
taimama ba, domin Allah bai dorawa rai sai abinda zata iya.
Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar
farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan taimamar. Idan mutum ya yi
taimama ya yi sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi kuma gashi ba
abinda ya karya mishi taimama to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar,
domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa idan bai samu ba to sai ya yi
taimama.
Idan mutum ana binshi wadansu salloli da ya
manta da su to ya samu ya sallacesu da taimama guda.
Kammalawa: wannan kadan kenan
daga cikin abubuwan da suka shafi taimama da fatan sun wadatar, kuma za'a koma
ga malamai.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna Jahar Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
No comments:
Post a Comment