Gabatarwa: Da sunan Allah
Mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga
fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da
Sahabban shi baki daya. Bayan haka a yanzu kuma muna daukene da abinda ya shafi
jerin hukunce hukuncen jinin biki wanda ake kira jinin haihua wanda yake da
izinin Allah bayanshi za mu kawo a wannan karon bayan da abayanan da suka
gabata muka kawo bayanai akan jinin al'ada.
Menene Jinni Biki: Jinine da yake
fitowa daga mahaiffa ta sanadiyyar haihuwa. Kenan shi jinin biki jinine da yake
da alaka da haihuwa, idan mace taga jini kwana daya ko biyu kafin haihuwa to
shima malamai suna lissafashi cikin jinin haihuwa.
Mafiyawan Kwanakinsa: Mafi yawan
kwanakin da macan data haihu zata ga jinin haihuwa malamai sun karawa juna
sani, wadansu sukace kwanaki ar'bainne (40), wadansu kuma sukace kwanaki
sittinne (60) kamar yadda mai Akhdari ya bayyana. Sabanin na al'ada shi kwanaki
goma sha-biyarne.
Idan mace ta haihu sai jinin bai dauke ba to
zata jira kwanaki arba'in, ko sittin, idan ya dauke a kwanakin shikenan sai ta yi wankan tsarki na daukewar
jinin haihuwa ta ci gaba da sallah da kuma sauran ayyuka na ibada, idan kuma
bai daukeba to sai a nemi magani ya zama jinin ciwo sai ta yi wankan tsarki ta
ci gaba da ibada, idan kuma jinin ya dauke kafin kwanakin kamar ya dauke ranar
da aka yi haihuwar to annan ma zata yi wankana ta ci gaba da sallah, laifine
maigirman gaske mace jinin haihuwarta ya dauke amma taki yin sallah wai sai ta
yi arba'in wannan ba tsari bane na addinin musulunci, domin tsarin musulunci
dazarar jinin yananan kafin kwanaki arba'in to dazarar ba za'a yi sallah ba,
amma dazarar jini ya dauke ko kafin sunane to dazarar za'a ci gaba da sallah,
sai a kiyaye.
Imam
Tirmizi yake cewa: Malamai sun yi ijima'i tun daga Sahabbai da Tabi'ai da
wadanda suka zo bayansu (Sun yi ijima'i) akan cewa lalle mace mai haihuwa zata
bar salla tsawon kwanaki arba'in sai dai idan ta ga tsarki kafin hakan (kafin
kwanaki arba'in din) sai ta yi wanka ta kuma yi sallah.
Idan mace ta yi bari sai ya zamana halittar
mutum ta bayyana a barin kamar ace ga tsarin halittar ba wai gudan jini bane ya
zamana kuma akwai jini day a zuba to anan tana da hukuncin jinin biki jinin
haihuwa, gwar gwadon kwanakin da asune ahalittar take bayyana a ciki sune
watanni ukune galibi ammadai mafi karanci sune kwanaki tamanin (80).
Idan ta yi barin gudan jini ko gudan tsoka ta
yadda halittar mutum bata bayyanaba to ba'a la'akari da wannan jinin da ya zubo,
saboda haka ba zatabar sallah ba kuma ba zatabar azumiba saboda jinin domin
bata da hukuncin jinin biki.
Idan jinin haihuwa ya dauke kafin wadancan
kwanakin da aka yi bayaninsu to zata yi wankane ta kuma yi sallah ko da jinin
ya daukene a ranar da aka yi haihuwar, to idan jinin ya dauke kafin wadancan
kwanakin sai kuma ya dawo to sai mu tsaya mu gani idan tsakani daukewar da
dawowar ya kai kwanaki goma sha-biyar zuwa abinda ya yi sama to wanda ya
dawodin jinin al'adane bana biki bane, amma idan tazarar batakai kwanaki goma
shabiyarba to jinin da ya dawo cikon jinin haihuwane.
Abubuwan Da Basu
Halatta Ga Mai Jinin Bikiba: Mu sani dukkan abuwan da jinin al'ada yake
hanawa ayiwa mai al'ada to jinin haihuwama yana hanawa a yi wa mai biki, haka
namma abinda jinin al'ada yake hanawa mai al'adar ta yi to jinin haihuwama yana
hanawa ta yi, kamar: Saki, saduwa, taba Alkur'ani, zama a masallaci dadai
sauransu kamar yadda bayani ya gabata a jinin al'ada.
Haka
namma kamar yadda ya halatta mai al'ada ta yi kunzugu megidanta ya shasshafata
ya taba ko ina a jikinta in banda daga cikibiya zuwa gwiwa to haka namma ya
halatta ga mai jinin haihuwa.
Kammalawa: Daga
wadannan takaitattun bayanai da suka gabata ya bayyana a fili cewa al'amarin
jinin haihuwa ba abune da za'a yi wasa akansaba, watakila hankali ya tafi kan
bukukuwa suna maijego kuma bata sallah kuma ga shi jinni ya dauke, kuma mun
fahimci munin tsohuwar al'adar nan na cewa maijego sai ta yi arba'in kafin ta
fara sallah ashe al'amari da bashi da alaka da addinin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna
Jahar Neja, Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Enter your comment...toh idan mutum yaga jinin ya dauke amma wani ruwa na fita shi ba fari ba yayi
ReplyDeleteyellow yazai yi dan Allah koshima sine din daukewa ne??
ALLAH YASAKA DA ALKAIRI
ReplyDeleteSHIN MACE NA IYA SAMUN CIKI YAYIN JININ BIKI
ReplyDeleteSHIN MACE NA IYA SAMUN CIKI YAYIN JININ BIKI
ReplyDeleteSHIN MACE NA IYA SAMUN CIKI YAYIN JININ BIKI
ReplyDeleteMasha allahu Akramikallah Allah ya saka da alkhairi
ReplyDeleteAFK Arena Tier List the top best heroes in the game to focus on at the very beginning and to the till end. Let's have a look at our AFK Arena.
ReplyDeleteAFK Arena Before beginning the game, you should know all the details about your heroes. For the different stages, like early, mid.
Find the best heroes for your team in this AFK Arena tier list. Heroes are ranked based on how useful they are and how much value they bring.
https://afkarenatierlist.com
Download Dragon City Apk Latest Version For Android. social point Download Dragon City Apk. Mod Any Game Using Lucky Patcher For Android!
ReplyDeleteyour blog color is wonderful.https://thesims4cheats.com/the-sims-freeplay-cheats/ Thanks for sharing idea.
ReplyDeleteAlong these lines, in the event that you are looking for a 3D game about going for Android and iOS gadget, at that point, Pixel Gun 3D is the thing that we'll be discussing in this article.
ReplyDeletewww.pixelgun3dgame.com/best-pixel-gun-3d-guns/
Masha Allah,Allah ya kara wa Malam lafiya da basira.
ReplyDeleteMashaaAllaah, jazakumullaah Khairaan.
ReplyDeletetoh idan mutum yaga jinin ya dauke amma wani ruwa na fita shi ba fari ba yayi
ReplyDeleteyellow yazai yi dan Allah koshima sine din daukewa ne?