Thursday, August 15, 2013
Tuesday, April 2, 2013
004- ABUBUWA MASU TSARKI
Bayanda a darasin da ya gabata aka
kawo bayanai da suka shafi abubuwan da suke su karankansu najasane, a yanzu
za'a kawo abubuwan da suke masu tsarkine.
Kandagarki:
Mu sani cewa abubuwan da suke kadan
sune suke da saukin lissafawa, amma abubuwan da suke da yawa akwai matukar
wahala a lissafesu, shi yasa aka lissafa abubuwan da suke najasa amma lissafa
abubuwan da suke da tsarki zai yi wahala. Annan za'a bada wadansu ka'idojine da
za su taimaka maka kwarai da gasket wurin tantance najasa ko rashinta, sannan
kuma za'a lissafa wadansu abubuwan da za'a iya ganinsu kamar najasane alhali
kuma ba najasa bane.
Ka'idoji:
(1) Kasa: Duk inda doron
kasane kake so ka ibada sai kake ganini kamar akwai najasa ko babu to asali
shine babu najasar banda: bola, mayanka, bandaki da makabarta domin ba'a sallah
a ita.
(2) Dutse: Hakanan dutse ko
kamfa kake kokwanton yana da najasa ko bai da ita, to asali shine bai da
najasa, sai ka sami tabbas in kuma baka samu ba to ka yi ibadarka wurin mai
tsarkine.
(3) Tufafi: Shima alokacin da
samu kanka cikin kokwaniton yana da tsarki ko baida tsarki kuma baka sami tabbas
hakaba to sai ka koma asali shine mai tsarki ne, sai ka yi ibadarka da shi.
(4) Ruwa: Asali akan ruwa
shine mai tsarkine har sai an sami tabbataccan dalili akan canzawar launinsa ko
dandanonsa ko shisshinarsa, saboda haka dazarar an baka ruwa kada ka tsaya kai
ta tambaya sai ka yi hukunci da wadannan abubuwan da suka gabata, domin kada ka
je ka cika tambaya ka haramtarwa da kanka ruwan ba tare da wani dalili
shar'antacceba, Umar dan Khattab (Allah Ya kara masa yarda) sun biyo ta gidan
wata mata da musulma bace ta fito musu da ruwa sai abokin tafiyar ta Umar ya
kama tambaya kan ruwan sai Umar hanashi.
Abubuwa Masu
Tsarki:
Na daya: Gawar mutum. Na biyu:
Gumi/Zuffarsa. Na uku: Yawun mutum. Na hudu: Majinarsa. Na biyar: Hawayensa. Na
shida: Kwai muddindai bai zama biragurbiba (wato mai wari). Nonon mutum. Na
bakwai: Nonon dabbobin da ya halatta a ci, kamar saniya rakuma, akuya…'. Na
takwas: Fitsari da Kashi na dabbobin da basa cin najasa, kamar fitsarin saniya da
na akuya, rago muddin dai ba sacin najasa, kenan ya halatta asha ko ashafa
kamar yadda akan idan kazzuwa ta kama mutum domin ba najasa ba ne, kamar yadda
wadansu mutane suka zo wurin Ma'aikin Allah suna fama da wasu cututtuka 'sai ya
tura su wurin da ake daure rakuman sadaka da su sha fitsarin rakuman da nonon
su, amma sauran dabbobi fitarinsu da kashinsu yana bin hukuncin namanne, idan
cin namansu halasne to fitsarinsu da kashinsu ba najasa bane. Haka namma
ragowar ruwan da suka sha, da abincin da suka rage, idan bai halatta cin
namansu ba to ragowar ruwansu da abincinsu ya zama najasa, kamar kare,
jaki,alade….'. Na tara: mataccan abinda
bai da jijni mai gudana a jikinsa, kamar: kuda, tururuwa. Hakanamma laima-laimar da ke a gaban mata wanda yake ba wadanda aka ambata ba, domin dakyar za'a rasa laima a gaban mace.
Shi kuma maniyyi mun yi Magana yadda malamai suka karawa juna sani
akanshi, amma zance mafi karfin dalili shi ne 'maniyyi ba najasa bane' kamar
yadda Abdullahi bn Abbas yace ''Aikamar majina ne''. Amma kuma idan ya fita ya
zama wajibi a yi wanka, shi kuma maziyyi ba a yi masa wanka saidai tsarki.
Kammalawa: Daga wadannan
bayanai da suka gabata mun kara fahimtar abubuwan da suke ba najasa bane ko da
ko ka kyamace su, amma kuma hakan ba ya sa mutum ya barsu a jiki, domin ita
tsafta cikon addinice kamar yadda bayanai za su zo akan haka a rubutu na gaba.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
003- NAJASA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA
Bayanda a darasin da ya gabata aka
kawo bayanai da suka shafi ruwa, a yanzu za'a kawo abubuwan da ake yi da ruwan,
akan haka za'a fara da najasa da yadda ake gusar da ita da ruwa da sauran
hukunce hukuncen ita najasar, Allah Ya yi mana jagora amin.
Abubuwan Da Suke
Najasa:
Na farko: Fitsari. (Na mutum) Na
babba ko na karami na mace ko na namiji, ya fara cin abinci ko bai faraba. Na
biyu: Bayangida (Kashi na mutum). Na uku: Mushe, shine abinda ya mutu da karan
kansa, ko aka yankashi ta hanyar da bata musulunci ba. Na hudu: Nonon dabbar da
ta yi mushe. Na biyar: Nonon dabbar da aka haramta cin ta, kamar nonon karya,
ko alade ko jaka...' Na shida: Fitsarin dabbar da aka haramta cin ta, kamar
fitsarin jaki, ko kare…' Na bakwai: Kashin dukkanin dabbar da aka harantata,
kamar kashin alade (alhanzir), kashin jaka/jaki..' Na takwas: Kashi da fitsari
na dukkanin dabbar da take cin najasa. Na tara: Giya. Na goma: Jini, saboda
haka bai halatta a tari jinin da aka yanka dabba ba wai ace za'a gasa shi ko a
soya ko ayiwa dabbobi abinci da shi ba domin najasa ne (in banda jinin da ake
samu a cikin dabba bayan anyankata wanda bai fitaba, ai dakyar a rasa jini a
cikin dabba). Na sha-daya: Ruwan ciwo. Na sha-biyu: Maziyyi, shi kuma ruwane da
yake fari yana da laushi yana fitane lokacin motsawar sha'awa ta mace ko namiji
ta hanyar wasa ko kallo ko nitsewa cikin tunani, amma idan sha'awa ta kara
karkafafa to maniyyine ke fita, shi kuma maniyyi ana jin fitarshi sabanin maziyyi,
sannan shi kuma maniyyi yana da kauri sabanin maziyyi shi yana da laushine,
bayanai za su zo akan shi nan gaba kada idan Allah Ya yarda. Na sha-uku:
Wadiyyi, shi kuma ruwane fari yana kauri sau da yawa yana fine akarshen
fitsari, ta sanadiyyar daukar kaya mai nauyi, ko matsanancin sanyi, ko kullewar
ciki. Na sha-hudu: Ragowar ruwa ko aminci na dabbar da ba'a ci, kamar rowan da
jaki ya sha ya raje, in banda mage. Na goma sha-biyar: Yawun kare da na alade,
ko na dukkan babbar da ta samu ta hanyar su. Na goma sha-shida: Amai, alokacin
da canza daga yanayin abinci, kenan idan aka ci abin ci yanzu sai kuma aka
harar da shi wannan harawwar ba najasa bace. Wadannan sune abubuwan da suke
najasa, amma akwai wadansu da malamai suka karawa juna sani akansu kan najasa
ne ko ba najasa ne ba, kamar ragowar ruwa na wanda ba musulmi bane ya sha,
hakanan akan maniyyi.
Shidai Maniyyi na namiji: Ruwa ne da yake fari maikauri yana tunkudar
junansa alokacin da zai fita, idan ka shinshina shi ya yi kama da hudar dabino,
kuma ya yi kusa da kanshin kulli, amma idan ya bushe yana kasancewa kamar
karnin fasasshan kwai. Wannan shine galibin yadda maniyyin namiji yake
kasancewa, wani lokacin ya kanzo sabanin wadannan bayanai da suka gabata. Yana
fitane lokacin matsananciyar sha'awa ta sanadiyyar kallo ko wasa ko matsanancin
tunani ko lokacin saduwa. Shi kuma Maniyyin mace, shi ma: Ruwane fatsi-fatsi
yana da laushi. Wannan ya tabbatar da cewa mace ma tana da maniyyi kuma da shi
ne da na namiji Allah Yake halitta da su.
Wasu malamai sunce maniyyi najasa ne domin yana fitane ta mafitar
fitsari wanda yake shi kuma fitsari najasane, wasu malaman kuma sukace ba
najasa bane domin da shi ne Allah Ya halicci dan'adam kuma a cikinsu akwai
Annabawa da Manzanni, kenan ya za'a mutum da Allah ya karramashi da yaukaka shi
har ya fitar da Annabawa da Manzanni ace kuma da najasa aka yi shi??. Wadannan
sune abubuwan da suke najasa da kuma wadanda malamai suka yi wa juna Karin
fahimta.
Hukuncin Najasa:
Wajibine gusar da najasa daga jiki da tufafi da wurin da za'a yi sallah,
idan mutum yana da ikon gusar da ita kuma yana sane bai gusar da ita dinba ya
yi sallah da ita to ba shi da sallah. Addinin musulunci addinin tsaftane abinda
musulunci yake so shine akoda yaushe ka sance cikin tsarki, mafificin tsarki
kuma shi ne tsarkin zuciya a kakkabeta daga barin shirka da zalinci da hassada
da munafunci da dukkan wata mummunar dabi'a, idan aka samu tsarkin zuciya kuma
ga tsarkin tufafi da ganganjiki da kuma mahalli to lalle wannan shi ke nuna
kammaluwar mutum.
Yadda Ake Gusar Da
Najasa:
Idan ka ga inda najasar take a jikinka ko a tufafinka to iya inda yake
iya nan zaka kama ka wanke, sabanin yadda wasu matan suke yi wai dukkanin
tufafin da tasa alokaci da take al'ada to sai ta wanke su, kama daga dankwali
da zani da riga…' wannan musulunci bai zo da shi ba, inda kwai kika ga jini iya
nan kawai za ki wanke. Idan kuma najasar ta rikice maka baka ganta ba, amma ka
tabbata akwaita ajikin tufafin na ka shikenan sai ka wanke tufafin gabadaya. Amma
idan najasa ta fantsamo sai kake kokwanton ta tabaka ko bata taba ka ba, kuma
kai baka ganta ba kuma ka duba mai Ahlari yace sai ka yayyafa ruwa a wurin.
Amma kuma idan wani abu ya fallatso maka sai kake kokwanto wannan abun
najasane ko ba najasa ba ne, to awannan lokaci ba wani hukunci akanka, ba yayyafa
ruwa ballantana wankewa, domin mafiyawan abubuwa masu tsarki ne, najasa kadanne
shi yasa ake iya lissafe su.
Idan inda najasar take kuma filine ko bango ko wani dutse sai aka yi ruwan
sama ko kuma aka kwarara ruwa mai tsarki akai shikenen an gusar da wannan
najasar. Amma idan ta kasace yawun karene wato karene ya baki a kwano ko a
kwarya to za'a zubar da abinda yake ciki sannan a wanke sau bakwai sannan asa
kasa a daya daga cikin bakwai din. Amma najasar da ba wannan ba sai a wanke ya
wanku sabanin yadda ake yi, da yaro ya yi fitsari sai ace wai za'a yayyafa ruwa
alhali wankewa akace a yi, wani ruwamma da aka yayyafa kamar karawa fitsarin
yawa aka yi, Allah ya sawwake. Ya zama wajibi a tshi tsaye a gusar da najasa a
tsaftace muhalli, musulmi ya kasance tsaftattace tsafta cikon addini ai ta fi
ace ita ciko ce, ita sharadice sai mutum ya tsarkaka daga wadannan najasar
ibadar shi zata karbu.
Abubuwan Da Najasa
Take Hanawa:
Anan za'a anbaci wadansu abubuwa ne
da basu halatta ga dukkan mara tsarki ya aikata su saboda darajarsu da
matsayinsu, kuma hadasin babbane ko karami, wadannan abubuwa sune:
(1) Taba Alkur'ani: Bai halatta ga
mara tsarki ya taba Alkur'ani, har sai ya yi tsarki inda so samune ma ya yi
alwala musamman idan ya kasance ba mai yawan daukan Alkur'ani bane.
(2) Sllah: Hakanan bai
halatta ga mara tsaki ya yi sallah ba farillace ko nafila, har sai ya tsarkaka
ya kuma yi alwala, kamar yadda Ma'aikin Allah-tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi- yace: '' Allah ba zai karbi sallar wanda ya yi hadasiba har
sai ya yi alwala'' Bukhari:135, Muslim:225. Hakanan kuma ko da mutum
yana da tsarki amma tufafinsa ko wurin sallar baida tsarki to delene ya
tsarkake su kafin fara sallar, saidai idan bai saniba ko ya manta cewa a
tufafinsa ko wurin da ya yi sallah akwai najasa sai kuma da lokacin sallar ya
fita sannan ya gani ko ya tuna to anan ba komai sallar shi ta yi.
(3) Tawafi: Kuma dukkan
mutumin da bashi da tsarki to bai halatta ya yi Tawafin Ka'aba ba, daman kuma
ananne kadai ake dawafi a sararin duniyar nan.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata munsan abubuwan
da suke najasa ta yadda ko yanzu akace ka kawo biyar zaka iya cikin gaggawa, da
kuma hanyoyin da akebi wurin gusar da wannan najasa, wanda yake gusar da ita
din wajibine domin munji abubuwan da bai halatta mara tsarki ya yi ba, akaro na
gaba zamu kawo bayanai akan wadansu abubuwa da ake ganinsu kamar najasane
alhali kuma ba najasa bane.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Sunday, March 24, 2013
002- HUKUN-HUKUNCEN RUWA (RUWA ABOKIN AIKI)
Kada ka manta sallah itace shisshike na biyu daga cikin shikashikan
musulunci guda biyar, itace kuma ginshikin addinin musulunci duk wanda ya
tsaida ita to ya tsayar da addini, haka kuma duk wanda yabar sallah to yabar
addini. Ita kuma sallah bata zama sallah sai idan an yi alwala, an tsarkaka
daga dukkanin najasa an gusar da hadasi da kuma kabasi, wato dukkanin najasar
da ta fito daga jiki ita ake kira Hadasi, kamar mutum ya yi: fitsari,
bayangida, maziyyi…'' shikuma kabasi shine dukkanin najasar da ta shafi
jikinka, ko tufafinka, ko kuma wurin sallah. Gusar da wadannan abubuwa na
hadasi da kuma kabasi da aiwatar da alwala, basa tabbata sai da ruwa mai tsarki
kuma mai tsarkakewa, wato kenan rowan sai ya cika sharudda biyu, na farko ya
zama mai tsarki, na biyu kuma ya zama zai iya tsarkake wani.
Allah madaukakin sarki yana cewa ''Kuma mun saukar da ruwa daga
sama wanda za'a yi tsarki da shi'' Suratl Furkan, aya ta:48.
Wannan ayar tana kunshe da hukunce hukunce da dama, daga ciki akwa:
Allah ya sanya ruwa shine abinda za'ayi tsarki da shi, ba'ayi da yawu/miyau,
abunmamaki sai mutum ya gama fitsa sai lakato yawunsa ya goga abansa, lalle
wannan ya yi nesa da makaranta. Abu na biyu kuma shine ruwan sama ruwane da
za'a yi tsarki da shi kai tsaye, abu na uku dukkan ruwan da yake a cikakkiyar
siffarsa ta ruwa babu abinda ya canza shi to za'a yi tsarki da shi.
Abubuwan Da Suke
Canza Ruwa. Abubuwan da suke canza ruwa har ya zama wannan ba za'a yi
ibada da shi ba (kamar alwala, tsarki..) abubuwane guda uku, da zarar ruwa ya
canza da daya daga cikinsu to wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba, wadannan
abubuwa sune:
(1) Launi: Kazarar kalar ruwa
ta canza ba yadda aka san ruwaba, ko dai ya yi canza ya yi ja, ko baki, ko
kore…' to wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba.
(2) Dandano: Idan dandanon ruwa
ya canza to wannan ruwan ba za'a yi ibada dashi ba.
(3) Shinshina: Hakana duk abinda
ya jirta kanshin ruwa zuwa wani abu daban to wannan ruwan ba za'a yi ibada da
shi ba.
Idan ruwa ya canza da yada daga cikin wadancan
abubuwa uku kenan wadannan abubuwa sun jirkita shi ta yadda ba zai iya amsa
sunan ruwaba, domin ya zama Sobo (Zobo) ko kunu ko ruwannan datti, to wannan
ruwan ba za'a yi ibada da shiba. Amma idan daya daga cikinsu ya fada cikin ruwa
amma bai canza ruwanba ta dayan wadancan fuskoki uku to babu abinda ya sami ruwan
za'a yi aiki da shi, kuma za'a ibada da shi. Wannan zai nuna kuskren da ake yi
na idan ansa hannu a ruwa ko mutum ya tara fanfo sai kasa hannu ko kasa kwano
ko buta sai ace za'a malalar da ruwan wai bashi da tsarki, ko wata dabba da ake
ci (wacce ba ta cin najasa) ta sha, ko kuma dabba ta fada rijiya ko ma mutum
sai ace wai za'a kwashe ruwan rijiyar azubar (ko guga kaza) wannan duk bai halattaba a musulunci, duk
abinda ka ga ya cikin ruwa kuma ka cire shi ka ga babu abinda ya canza rowan
kwatakwata cikin wadancan abubuwa uku ka yi shiru da bakinka aci gaba da aiki
da ruwa.
Nau'ukan Abinda
Ruwa Yake Canzawa Da Su: Canzawar ruwa da muke Magana akanshi yana da kyau
musan abinda ruwa yake da canzawa da shi lura da hukunce-hukuncen kowanne,
kamar haka:
- Da Makwancinsa: Idan ruwa ya canza
kala ko dandano ko shinshina, saboda inda yake, kamar Jarkasa, Farar kasa,
Kanwa, Kainuwa, Gansakuka… duk wadannan idan ruwa ya canza ya yi fari saboda
wurin farar kasace ko ya yi Jaa saboda wurin jarkasace ko dandanonshi ya yi
gafi saboda wurin kanwace ko tekuce ko wuraran da ake hakar mai, duk wannan
canza wad a ruwa ya yi babu abinda ya shafeka zaka yi ibadarka da shi
salin-alin alattacciyar ibada.
Kenan waccar Magana da aka yi sai idan ruwan ya canza da wani abu na
daban da ba makwancinsaba ta yadda zai iya yuwuwa a rabasu amma a inda yake
makwancinsane babu yadda za'a yi ka rabasu.
- Abu Mai Tsarki: Idan wani abu mai
tsarki kamar gishiri ko yaji ko miya ko sabulu ya zuba cikin ruwa amma
kwatakwata bai canza ruwanba to wannan ruwan za'a yi ibada dashi kamar yadda
bayanai suka gabata, amma idan sun canza ruwane to wannan rowan ba za'a yi
ibada da shi ba, amma za'a yi ayyukan gida da shi, kamar girki wanki kunun-zaki
d.s.
- Najasa: Idan najasa ta
jirkita ruwa ta daya daga cikin abubuwannan uku, to bai halatta a yi anfani da
wannan rowan kwatakwata ba za'a yi ibada da shi ba, kuma ba za'a yi wasu ayyuka
nadaban da shiba kenan kwararar da shi kawai za'a yi.
Lalle wannan ya nuna mana muhimmacin ruwa da kuma yadda addinin
musulunci ruwa shine abinda ba yi za su ibada da shi bai sa musu feturba ko gas
domin rahamar Allah ga bayinsa sai ya sanya musu ruwa kuma ya sanya shi ya zama
sinadarin rayuwa. Saidai kawai idan mutum bai sami ruwaba a lokacinda zai yi
tsarki sai ya yi Istijmari, ko zai yi alwala kuma gashi babu ruwa sai ya yi
taimama, kamar yadda bayanansu zasu zo nan gaba.
Kammalawa: Daga wadannan
bayanai da suka gabata zai nuna baka yadda addinin musulunci ya baima ruwa
kulawa ya kuma sawwake shi, kuma wannan yana nuna mana yadda ya zama wajibi mu
tashi musan hukunce-hukuncen ruwa domin idan mutum bai sani ba sai ya debi ruwan
wanki ko kuma ruwan da ya gama wanka da shi bayan ya zama sabulu ya ce zai yi
tsarki da shi, domin wasu sun dauka ruwan alwala shi ake bashi wannan
hukunce-hukunce amma shi tsarki mutum zai iya yi da ko wanne, alhali abin ba
haka bane, Allah ya sawwake amin. Allah Shi ne masani.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
001- IBADA DA HUKUNCI
Gabatarwa: Dasunan Allah Mai
Rahama, mai jinkai, tsira da amincin Allah ya tabbata ga Ma'aikin Allah Annabi
Muhammad. Awannan lokacin da izinin Allah mai kowa mai komai muna fatan kawo
wadansu bayanaine na daban bayan kammala waccan doguwar salsala da take dauke
da wadansu abubuwa bakwai masu halakarwa. Wannan bayanai kuwa matashiyarsu
itace: Ibada Da Hukunci. Fatammu shine kawo bayanai filla-filla kan abinda ya
shafi hukunce-hukncen nau'ukan ibada kamar tsarki da rowan da ake tsarki da
shi, da kuma bayanai akan abinda yake najasa da alwala da abinda ke bata
alwalar ta taimama da wankan tsarki da abinda ke sa wankan, da huknce hukuncen
sallah, kamar sharuddan sallah lokutanta kiran sallah, salloli na farilla
nafilfili, tada ikama, kabaliyya da ba'adiyyah, hukunce-hukunce masallaci,
sallar kasaru. Hakanan muna fatan kawo bayan kan Azumi da Hajji d.s…gwargwadon
abinda Allah Ya hore, da fatan zamu tsaya musan Ibadar da Allah ya dora mana
kuma musan hukunce hukuncen wannan ibadar, Allah Ya yi mana jagora, amin summa
amin, asha karatu lafiya.
Ibada: Ma'anar ibada itace ''Gamamman sunane da ya tara
dukkanin abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi, na zantuttukane ko na
ayyuka na filine koko na zuciyane''.
Kenan ibada tana shiga ayyukan
gabbai kamar: Alwala, zakka Hajji, kamar yadda maganama ke shiga cikin ibada
kamar: Karatun Kur'ani, Salati ga Ma'aikin Allah, na bayyane kamar tsarki dana
boye kamar niyya.
Hukunci: idan akace hukunci
shine hukunce-hukuncen da shara'a ta na cewa abu kaza: Wajibine, ko Haramunne,
ko kuma Mustahabbine ko Makaruhine, ko kumama Halasne. Wadannan abubuwa biyar su ake kira da Ahkamus
Shar'iyyah At-Takleefiyyah. Kuma ga bayanansu da Shara'a ta yi:
(1) Wajibi: Shine abinda ana
bada lada ga duk wanda ya aikata shi akan an'umarceshi, kuma ana azabtar da duk
wanda ya barshi. Kamar salloli na farilla da tsarki da Azumin Ramadan…'
(2) Haramun: Shine abinda idan
mutum ya aikata shi za ayi masa ukuba, idan kuma ya barshi yana da lada. Kamar:
Sata, Zina, Luwadi, Shangiya.
(3) Musthabbi: Shine idan mutum
ya aikata za'a bashi lada, amma idan bai aikataba babu komai akansa. Kenan
aikata shi ya fi. Kamar daga hunnuwa a lokacin kabbarar harama, kamar karatun
mamu alokacin da liman yake karatunsa aboye.
(4) Makaruhi: Shine abinda idan
an barshi akwai lada, idan kuma an aikata babu ukuba, kenan barinshi ya fi.
Kamar susa ana sallah da dan waige kadan.
(5) Halas: Shine abinda idan
an aikata babu lada akan aikatshin da aka yi, hakanan idan an barshi babu lada
akan barin na shi da aka yi, kenan sai an kallaci niyyar da tasa aka yi ko aka
bari akan haka za'a sami lada ko zunubi. Kamar bacci, idan mutum ya yi bacci da
wuri domin ya tashi cikin dare ya yi nafilfili da addu'oi to wannan yana da
lada, hakanan idan ya yi bacci domin yaba jikinsa hakkinsa, tunda yazo a hadisi
jikinkama yana da hakki, to duk wadannan akwai lada. Idan kuma mutum ya yi
bacci alokacin da yasan indai ya yi bacci a wannan lokacin took zai iya rasa
sallah to ba'ayarda ya yi bacci a wannan lokacinba, shi yasa aka hana bacci
tsakanin Magariba da Lisha.
Wadannan sune hukunce hukunce da sune ake hukunci, kuma tananne ake
kaiwa inda za'a yi hukunci akan ibadar mutum ta yi ko bata yi ba, kenan dole mu
tashi tsaye musan yadda za mu yi ibadarmu yadda Mahaliccimmu ya umarcemu mu yi
ta harshen Annabinsa Annabi Muhammad -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi-, ka da mu yi sakaci mu da iyalammu da kannemmu da yayyammu… Allah ya yi
mana jagora amin.
Lalle tsayawa akan a fahimci wannan addini na musulunci yana cikin
mafiya kyawun ayyukan da Allah ke so, kuma alamace ta Allah na son mutum da
alheri, kamar Yadda Ma'aikin Allah -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi- yake cewa ((Duk wanda Allah yake nufinshi da alheri sai ya fahimtar da
addi)). Bukhari ya ruwaitoshi a hadisi na:71, Muslim kuma: 1027.
Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Shine
wanda Ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin da yake na gaskiya''
Suratut- Tauba: 33. Shiriyar Itace ilimi mai anfani, Addini na kwarai kuwa
shine: Ayyuka masu kyau.
Babu wata tantama tabbas yakama kafin mutum ya himmatu wurin aikata
kowanne irin aiki yasan hanyar day a kamata yabi domin aikin na shi ya zama ya
yi shi daidai, ta yadda zai yi ya sauke aikin da aka dora masa wanda zai zama
sanadiyyar tseratar da shi daga wuta da kuma shigarshi aljanna.
Akan Haka Mutane
Sun Kasu Kashi Uku:
(1) Wadanda suka hada ilimi mai
anfani da kuma aiki na kwarai. Wadannan sun rabauta duniniya da lahira, don
Allay ya yarda da su.
(2) Wadanda suka san ilimi mai
anfani amma basu yi aiki da shiba, wadannan sune wadanda Allah ya yi fushi da
su.
(3) Wadanda suke aiki tukuru amma ba
tare da ilimiba, wadannan sune batattu.
Kammalawa: Daga takaitaccan
wannan jawabi ya bayyana agaremu ashe ibada ta ka su kashi-kashi, akwai ta
kabbai, akwai ta zuciya akwai kuma ta zahiri, kuma ita ibada hanyace da mutum
zai sami yarda Mahaliccinshi domin yanayin abinda Mahaliccin ya yarda dashi,
amma duk wannan zai same su ne idan mutum ya bi karantarwar farin jakada
Ma'aikin Allah Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, kin yin aiki da
karantarwa yanasa Allah ya yi fushi da mutum, kamar kuma yin aiki ba akan
karantarwarba yana sa mutum ya kasance cikin batattu. Allah Ya tsaremu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu, Minna, Jahar Neja Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
Subscribe to:
Posts (Atom)