Sunday, March 24, 2013

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Yiwa Mace Mumina Kazafi)7/7#


Yiwa Mace Mumina Kazafi: A yanzu za mu yi bayani akan abu na bakwai kuma na karshe cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Yiwa Mace Mumina Kazafi.
Kazafi Shine: Jifan mutum da aikata alfasha ta zina, ko kore juna biyu ko ma Da ba tare da ya bayar cikakkun shaiduba.
       Alokacin da mutum ya jefa kanshi cikin irin wadannan halayya ta kazafi to lalle ya jefa kansa cikin halayyar da take halakarwa, domin yin kazafi ba karamin bala'ibane, alokacin da mutum ai wance mazinaciyace ko ya yi lalata da ita, ko wannan ciknnanata bana mijintabane ko danta/'yarta ai bana mijinta bane to lalle ya tsokano tsuliyar dodo dole ya kawo cikakkun shaidu na mutane hudu maza musulmai da zasu bada shaida akan hakan, idan kuma mai kawo shaiduba ko ya kawo basu cikaba to kowanne mutum gada cikinsu bulala tamanin (80) za'a yi masa, kamar yadda bayanai zasu zo nan gaba kadan.
       Wannan shiri da musulunci yake dashi bakaramin shiri bane domin kare mutunci, masu iya Magana na cewa mutunci madarane in ya zube bai kwasuwa, addinin musulunci yana daga cikin manyan manufofinsa kare mutunci, wannan yasa musulunci ya dauki irin wannan mataki musammamma 'ya mace, domin alokacin da aka bata mata suna to gaba daya anbata mata rayuwarta, shi yasa ayoyin da suka yi Magana akan kazafi sun anbaci macece basu anbaci namijiba wannanko ba wai dan hukuncin ya sha daban bane a'a hukuncin iri dayane ga duk wanda ya yi mace ko namiji kazafi, kuma bai iya kawo cikakkakun shaiduba, idan ko ya kawo shaidu da duk abinda Shara'a ke bukata suka cika to baza'a kira wannan da sunan kazafiba.
       Yiwa mace mumina kazafi bai halattaba kuma yana cikin abubuwan da suke halakarwa, saboda haka dadin fira ko kiyayya kada ta dauki mutum ya yiwa wata/wani kazafi ko yasa a yi.
Ayoyin Da Suka Yi Magana Akan Kazafi: Idan ka tsaya ka kalli ayoyin zaka gansu kashi ukune kuma duk suna cikin Suratun Nur.
Kashi Na Farko: Ayata: 4-5, Allah Madaukakin sarki yana cewa: ''Wadanda suke jifan mata masu kamunkai (da zina) sannan kuma basu kawo shaidu huduba to ku yi musu bulala tamanin (80), kuma kada ku sake karbar shaidarsu har abada, kuma waddan sune fasiakai. Saidai kawai wadanda suka tuba bayan haka kuma suka kyautata to lalle Allah mai yawan gafarane kuma mai yawan jinkai.''
    Anan Allah madaukakin sarki ya bayyana hukuncin duk mutumin da ya yiwa mace/namiji kazafi kuma bai iya kawo shaidu huduba sai Allah ya bayyana hukuncin da za'a yi masa. Abu na farko bulala tamanin (80), abu na biyu ba za'a sake karbar shaidarsaba har'abada, abu na uku kuma wannan mutumin fasikine. Sai idan ya tuba, to ananne malamai suke maganar shin inya tuba za'a ci gaba da karbar shaidarsa kuma shikenan shi ba fasiki bane? Amma ko ya tuba sai an yi mishi bulala tamanin.
Kashi Na Biyu: Ayoyin da suka yi bayanin maigidan da ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya kawo shaiduba to shi tsinuwa za su yi da matar ta shi, Allah Yana cewa:
''Wadanda kuma suke jifan matansu (da zina) kuma ya kasance basu da shaidu saidai karankansu, to shaidar dayansu (itace) Rantsuwa hudu da Allah lalle shi yana cikin masu gaskiya * (Rantsuwa) ta biyar tsinuwar Allah ta haukanshi in ya kasance cikin makaryata. * Kuma abinda zai hana ayi mata azaba (haddi) shine ta yi Rantsuwa hudu da Allah cewar lalle shi (mijin) yana cikin makaryata *. (Rantsuwa) ta biyar lalle fushin Allah ya tabbata akanta in (mijin nata) ya kasance cikin masu gaskiya'' Surartun Nur, ayata: 6-8.
Anan Allah madaukakin sarki ya yi bayanin idan miji ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya kawo shaidu huduba to 'Li'ani'' za su yi. Amma duk wanda ba miji bane to kodai ya kawo sahaidu mutane hudu maza musulmai ko kuma ayi mishi bulala tamanin, ba maganar shi wanda aka yiwa kazafi wai ya rantse idan ba haka bane, ko kuma shi da ya yi kazafin cewa ya rantse duk babu kodai shaidu ko bulala tamanin.
Kashi Na Uku: Ayoyin da suka yi Magana akan kazafin da aka yiwa mata muminai masu kamunkai natsattsu kammalallu to wadannan masu yiwa irin wadannan matan kazafi tsine musu aka yi duniya da lahira. Allah madaukakin sarki yana cewa:
 ''Lalle dukkanini wadanda ke jifan mata masu kamun kai gafalallu (daga aikata dukkanin alfasha) wadanda suke muminai to an tsine musu a duniya da kuma lahira, kuma suna da azaba maigirma* Aranar da harsunannu za su bada shaida akansu da hannayansu da kuma kafafuwansu ta sanadiyyar abinda suka kasance suna aikatawa* Awannan ranarce Allah zai cika musu sakamakonsu na gaskiya, kuma zasu sani lalle Allah shi wanda yake mai gaskiya kuma mai bayyanar da abubuwa''. Suratun Nur, ayata: 23-25.
Wannan ya nuna mana shi karankanshi kazafin ya kasu kashi-kashi, kashi na farko shine yiwa gama garin mutane wadanda suke suna da kyawawan halaye da kuma wanda ba'a rasaba, su aka anbaci hukunci yi musu kazafi a kashin farko, sai kuma wanda ya kasance tsakanin miji da mata. Sai wannan kashi na uku, wanda mutum zai ga mace/namiji mai kamun kai mai addini natsattse mumini kawai ya antayo ashar ya watsa mata/mashi ya dinga fadan wasu maganganu wanda da za'a tara mishi arzikin duniya domin ya kawo shaida akan haka ba zai iyaba. Domin wani ya dauka irin halin da yake dashi to kowa haka yake, to kaga bayan ya kasa kawo wadannan shaidu za'a yi masa hukuncin kazafi anan duniya sanna kuma ya jira ranar alkiyama, domin Allah baya bari a taba bayinsa na kwarai, Ya Allah ka samu daga cikinsu, ka karemu da sharrin masharranta ka tsaremu ka tsaremana imanimmu, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun bayananan ya bayyana agaremu yadda musulunci ya dauki mutunci da daraja da kima ya karewa kowa mutuncinsa musamman 'ya mace, domin idan ba hakaba sai kowa ya fadi abinda ya ga dama ko asashi ya fada yana ganin bai huce aci tararshiba, amma idan yasan zai sha bulalane to dole ya naba'a yasan me zai fada, sai yazama yak are mutuncinsa dana zuriyarsa kamar yadda yak are mutuncin wani dana ziriyarsa.
Annanne kuma muka zo karshen wannan silsila wacce take dauke da sharhin wannan hadisi da Abu Hurairata ya ruwaito daga wurin Ma'aikin Allah na wadannan abubuwa bakwai masu halakarwa, lalle ma'aikin Allah ya isar da manzanci kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, hakika ta'amuli da wadannan abubuwa tabbas yana halakarwa kuma wannan kowa ya gani ya tabbatar wannan zai kara imanine bisa imani. Akaro na gaba zamu kawo bayanne kuma wadanda zasu haskaka mana rayuwarmu da addininmu, Allah ya kaimu wannan lokacin ya hadamu da imani, aimn.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Juya Baya A Lokacin Yaki)6/7#

Ja-Da-Baya Lokacin Gumurzu: A yanzu za mu yi bayani akan abu na shida cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Juya Baya A Lokacin Yaki.
     Jihadi wani al'amarine da musulunci ya shar'antashi ya kuma tsarashi kamar yadda ya tsara rayuwar bil'adama ta duniya da kuma ta lahira. Ayoyi na Alkur'ani mai girma da ingantattun Hadisai Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- duk sun zayyana yadda jihadi yake hanan kuma malamai sun zayyana yadda yaki yake domin habbaka addinin Allah, kuma kamar sauran al'amura sai mutum ya yi kamar yadda aka shar'anta sannan zai sami ladanshi. Yaki domin habbaka addinin Allah shine kololuwar musulunci, kamar yadda Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya bayyana a Hadisin Mu'az.
    Kuma kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya bayyana a cikin Alkur'ani mai girma cewa: ''An wajabta muku yaki alhalin bakwasansa'' Bakara, ayata: 216.
   A wannan dogon hadisi da muke bayani a kanshi, Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa juyawa da nufin guduwa yana daga cikin abubuwa masu halakarwa domin kamar wannan juyawar da mayaki ya yi yana nufin a murkushe musulunci kenan.
   Amma juyawar da zata laifi sai idan yawan musulmai daidaine dana kafirai, ko kuma su wadanda ba musulmanba sun ninka musulmai ribinyi biyu, amma idan yawan wadanda ba musulmai ya ninka yawan musulmai sama da sau biyu to awannan lokaci babu laifi idan musulmi ya juya da baya kamar yadda aya Suratul Anfal ta yi nuni:
   ''Ayanzu Allah Ya sawwaka muku, kuma ya bayyanar da cewa a cikinku akwai masu rauni, idan an sami mutane dari daga cikinku masu hakuri zasu rinjayi mutane dari biyu (daga cikinsu), in kuma an sami mutane dubu daga cikinku zasu rinjayi dubu biyu (daga cikinsu) da izinin Allah, Allah Yana tare da masu hakuri. Ayata: 66.
      Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa ''Kada ku yi fatan haduwa da abokan gaba, ku roki Allah zaman lafiya, idan kuma har kuka hadu da su to ku tabbata, ku sani aljannah tana karkashin inuwar takobi''.
  Ya Allah muna rokonka ka zaunar da mu lafiya, kuma ka dawowa da musulunci izzarsa da kimarsa da darajassa.
Kammalawa: wannan ya nuna yadda musulunci bai yarda da juyawa da bayaba a lokacin da aka yi futo-na-fito, kuma mu sani annan ba wai ana bayanine akan abinda ya shafi hukunce-hukuncen yaki bane (Jihadi) wannan wurinsa daban malamai sun fayyace shi da yadda ya karkasu da matsayin ko wanne kaso daga cikinsu, amma anan an yi bayanine akan abinda ya shafi tserewane afagen fama. Ya Allah ka tsaremu ka tsare mana rayukammu da imanimmu. Amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, Minna, Jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com

Wednesday, March 13, 2013

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Cin Dukiyar Maraya)5/7#


Cin Dukiyar Maraya: A yanzu za mu yi bayani akan abu na biyar cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Cin Dukiyar Maraya.
Maraya: shine wanda mahaifinshi ya rasu kafin ya balaga ya yi hankali. Ma'aikin Allah ya ja kunnen al'umma sosai da sosai akan kulawa da hakkin maraya da tausaya masa, da fadi-tashi akan al'amuransa kuma ya bayyana falalar hakan awurare dadama. To amma abin takaici sai awayi-gari dan abinda uba ya mutu ya barwa 'ya'yansa sai wani/wasu subi takan wannan abinda aka bari kafin dan lokaci ane meshi a rasa. Allah madaukakin sarki yana cewa dangane da masu cin dukiyoyin marayu da zalunci: ''Lalle dukkanin wadanda suke cin dukiyoyin marayu da zalunci, abin sani kawai suna cin wutane a cikinsu, kuma da sannu za'a kona su a wuta wacce ake rurata'' Suratun Nisa'I, aya ta:10.
       Akwai hanyoyi da dama da mutane suke bi wurin cinye wannan dukiya ta maraya, wasu idan suna hurda da mutum sai ya zama akwai wasu kudadensa ko filayansa komadai wasu kadarori da yasan ba wanda ya sani sai shi, sai kawai ya yi shiru akansu ya ki fito da su in kuma ya ga suna da yawa ko za'a gane sai ya dan tsakuro wasu daga ciki sauran kuma ya yi shiru akansu, ana samun masu irin wannan mummunan hali cikin matan mamacin ko 'ya'yanshi ko abokanshi ko abokan cinikayyarsa d.s, wannan haramunne ko tantama babu kuma duk wanda ya yi irin wannan hali sai ya amayar da abinda ya ci a ranar alkima alokacin da hakan ba zai yi anfaniba.
      A wasu wuraren kuwa hukumomin yankinne –masu unguwanni da dagatai Hakimai (wadanda ake kira masu kasa) suke wadaka da abinda akabarwa magada said an abinda aka sammusu, gonakine ko fadamu ko madaime aka bari.
       A wani lokacin kuma shi malamin da kakira domin ya raba gado shine wanda zai kamfaci wani kaso mai tsoka yace wannan na masu rabone, ko kuma a zaga ta baya ahada baki dashi don ya karawa wani, waifa wanda zai yi fada akan wannan mummunan hali shine kuma zai zama ja-gaba, Allah ya sawwake.
       Awani jikon kuma 'ya'ya mata da matan mamacin sune za'ayi rabon gado amma kwatata-kwata basusan me aka rababa, ko dai 'yan-uwan mamacin su yi watsi da su ko kuma 'ya'ya maza su yi watsi da 'yan-uwansu 'ya'ya mata, ko kuma duk ba wannan ba wacce tafi 'ya'ya sai tai zamanta akan dukiyar kaji don rashin jin tsoron Allah wai ana cewa ba'a raba gado da mara 'ya'ya, sauda yawa wata irin kazantar da ake yi awurin rabon gado kare ba zai ci ba.
       Awani karon kuma shi wanda akaba dukiyar marayun ya kula da ita bayan an gama rabo shine zai hauta da casa kafin-kiftawa-da bisimillah ya hallaka dukiyar bakidayanta.
       Bai halatta a dankawa yara kanana dukirasu ta gadoba sai bayan sun cika sharudda guda biyu:
(1) Balaga: Dole kai da akaba dukiyar mamaci ka ci gaba da riketa kana jujjuyata ba zaka danka masaba sai ya balaga, ita kuma alamar mutum ya balaga alamace kamar haka:
(a) Mafarki: Alokacin day a yaro ko yarinya ta yi ko ya yi mafarkin ya sadu da mace ko macen an sadu da ita kuma mani ya fita, to daga wannan lokacin hukunce-hkuncen shara'a sun haukanshi ko kanta mala'iku za su dinga rubuta musu ayyukan da kowa ya yi mekyau ko mara kyau sun yi aure ko ba su yi aureba domin babu wanda yace sai mutum ya yi aure sannan za'a bude masa fayil a wurin Allah. Ko kuma maniyyin ya fita a farke ba wai sai abacciba kadai.
(b) Bayyanar Gashin Mara: Hakanan idan gashin mara mai kaush-kaushi ya bayyana a gaban 'Ya mace ko Da namiji.
(C) Jinin Al'ada: Hakanan daga lokacin da mace ta ga jinin al'ada to daga wannan lokaci ta balaga hukunce-hukuncen Allah sun hau kanta, anan nake cewa dolene iyaye su tashi tsaye wurin kula da 'ya'yansu.
(d) Cika shekara 15: Alokacin da Dan amiji ya cika shekara 15 ko 17 ko 18, kamar yadda malamai suka karawa juna sani to lalle ya balaga.
  Wadannan alamun balaga ko wacce daya cingashin kanta take yi, ba lalle bane cewa sai sun bayyana duka, alokacin da daya ta bayyana shekenan, kuma ya zama dole iyaye da masu ruko su kula sosai da sosai, domin sai kaga yaro ko yarinya sun sha azumi amma kwatakwata ba maganr ramawa wai andauka sai anyi aure sannan mutum zai dinga cika ibadarsa.
(2) Sharadi Na Biyu Wayau: Koda yaron da kake kulawa da dukiya  ya balaga to bai halatta ka bashi dukiyarba sai ka jarraba hankalinsa da dabararsa da wayonsa, idan ya natsu sai ka danka masa, idan kuwa bai natsuba to bai halatta ka bashiba.
Wadannan sharudda guda biyu sune aya ta: 6 cikin Suratun Nisa'I ta yi bayani, Allah madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma ku jarraba marayu har idan suka isa aure to idan kun tabbatar da wayonsu sai ku ba su dukiyoyinsu, kada ku ci ita (dukiyar) da barna da gaggawa kafin su girma (komai yak are), duk wanda yake mawadacine to ya kame, wandako fakirine (marashine) to ya ci gwargwadon wahalarsa, idan zaku danka musu (dukiyar) to ku kafa musu sahaida, lalle Allah Ya isa mai lissafi akan komai''.
Wannan babbar ayace akan abinda ya shafi kulawa da dukiyar maraya a tsari mai cike da adalci da tausawa da baima kowa hakkinsa. Da farkodai ayar ta yi nuni da adinga jarraba su marayun har idan aka ga sun cika wadancan sharudda biyu sai aba su dukiyarsu, sannan ayar ta ja kunnen masu kula da dukiyar da kada su tasata a gaba da ci ham-ham kafin yara su girma babu komai, sai ayar ta bayya hakkin mai kula da dukiyar idan shi mai kula da dukiyar maraya dama mawadacine yana da harkokinshi to ya ci gaba da kulawa da amma ya kame daga cin wani abu na dukiyar, idan ko talaka kulawa da dukiyar marayan ta shagaltar da shi daga nashi fadi-ta-shin, to ya dauki gwargwadon wahalarsa, ma'ana inda wani kadauka aiki yake kulama da dukiyarka nawa zaka bashi, to abinda kasan zaka bashi haka zaka dauka.
     Sannan ayar ta nuna mana cewa idan lokacin dankawa maraya dukiyarsa ya yi kada ku kunshe kanku a daki a'a ku kafa shaidu, to kenamma a lokacin da zaka karbi dukiyar maraya ka tabbatar ansa shaidu kuma a rubuta adadin abinda ka rike, kada ka yarda ace ai ba sai anrubutaba ba danka bane, sauda yawa mutum ba zai raka kaba yace dare ya yi ma, wasu su za su zugo maryun bayan sun girma ace babanku yabar muku abukaza da abu kaza a nemi a hada ka fada da 'ya'yan kaninka ko yayanka, Allah Ya sawwake, sannan wurin shaidun ba lalle bane ace sai dattijai a hada da matasa wada suke da wayau Allah ne dai kadai yasan gawar fari.
Sai Allah Ya rufe ayar da ya isa ya zama mai lissafi, wannan yana nuna mana cewa a tsaya ayi lissafi mai kyau lokacin karba da kuma lokacin bayarwa, zaka lissafa duk abinda kake kashewa marayan dake hannunka kamar kudin makaranta, kudin koyon sana'a, domin zaka tsayane ka kula da tarbiyyarsa lokacin muzurai ayi mishi muzurai, lokacin fada ayi mishi fada in ya yi abin duka adoke shi amma ba duka mai tsananiba, domin sai an rintse ido akeshan magani musamman a rirn wannan lokaci ta tarbiyya ta sukurkuce. Kasa shi makarantar Islamiyyah data book da koyon sana'a, sai kaga ya girma ya zama natsattsen mutum kamili, ga kuma irin wannan dinbin lada da kasamu, domin duk wadannan al'amurra da kake wa wannan maraya kana da lada na musamman awurin Allah.
Ayoyin Alkur'ani mai girma sun zo da bayanin kada ku yi kusa da dukiyar maraya said a abinda yake shine mafi kyau, saboda yadda ayoyi suke Magana akan dukiyar maraya saida yakai wasu sun nemi su ware dukiyarsu data maraya ba tare da sun hadaba koda ko jinsinsu guda kamar dabbobi kayan gona kudi d.s, a Suratul Bakara aya ta: 220, Allah madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma suna tambayarka dankane da marayu, kace: Kyautata musu shine daidai, har idan kuka hada (dukiyarku da ta su ai 'yan-uwankune (ba komai), Allah Yasan mabarnaci kuma ya san mai gyara''.
Kuma ya kamata al'umma su tsaya su yi karatun-ta natsu akan marayu bai gagara mutum shima ya mutu ya bar na shi yaran kanana  ai shima ba zai so abinda ya bar musu wani ya yi wadaka da shiba.
Saboda haka lissafa cin dukiyar maraya ba-gaira-ba sabab da Ma'aikin Allah ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa ba karamin tashin hankali bane
Kammalawa: Awannan takaitaccan bayani day a gabata lalle munsan irin hakkin da maraya yake da shi, da kuma wajibcin tsayawa tsayin-daka akan akula da dukiyar maraya, sannan da bayanin minzalin da maraya zai kai sannan a danka masa dukiyarsa, sannan da bayanin cewa wannan aiki ba karamin matsayi yake da shi a wurin Allah ba, wannan kuma zai dada fayyace mana yadda musulunci a kullum yake kulawa da masu rauni, sannan ga shi yadda bayani ya gabata wadanda suka fi shan wahala sune mata da kananan yara, kuma ga yadda Allah Ya yi bayani akan dukkan mai cin dukiyar maraya da zalinci to wuta yake cima cikinsa, Allah Ya tsaremu kuma dukkan wadanda suke kula da marayun dake hannunsu ya Allah ka taimaka musu wurin sauke wannan nauyi, kuma Ya Allah ladan da kake baiwa wadanda suke kulawa da marayu ya Allah ka tabbatar mana mu da su baki daya, Amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
 Minna, jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
: munbarin musulunci

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Riba/Kudin-ruwa)4/7#



RIBA/KUDIN-RUWA: A yanzu za mu yi bayani akan abu na hudu cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu kuwa itace Riba/Kudin-Ruwa/Bashi da ruwa.
Mecece Riba?:
Ashar'ance Riba Itace: Kari akan wadansu abubuwa kebantattu.
Tsoratarwa A Kan Mu'amala Da Riba:
Ayoyi masu tarin yawa sunyi bayanin narkon azabar da Allah madaukakin sarki ya tanadar mai mu'amala da riba, hakanan Ma'aikin Allah Ya yi bayanin haka harma gashi ya lissafa riba cikin abubuwan da suka halakar da maita'amuli da riba, Allah Ya tsaremu amin.
Allah madaukain sarki yana cewa ''Duk wadanda suke cin riba bazasu taba tashi ba (daga kabarinsu) saidai kamar wanda aljan ya shafeshi, abinda ya sa haka saboda su (masu mu'amala da riba) sunce ai abinsani kawai kasuwanci kamar ribane, kuma Allah Ya halasta kasuwanci kuma Ya haramta riba, to duk wanda wa'azi ya zo masa daga wurin Ubangijinsa sai ya hanu (daga ta'amuli da riba) to yana da abinda ya wuce, kuma (sauran) al'amarinsa yana wurin Allah, amma duk wadanda suka ci gaba (da mu'amala da riba) to wadannan sune 'yanwuta kuma wadanda zasu dawwama acikinta* Allah Yana kwashe albarka (daga dukiyar da ake) mu'amalar riba da ita, kuma (Allah) Yana rainon sadaka, kuma (Shi) Allah bayason dukkan maiyawan kafirci kuma mai laifi''. Bakara, aya ta:275-276.
Lalle wadannan ayoyi guda sun yi bayanin yadda Allah ya kyamaci riba Ya haramtata kuma Ya yaye shubuhar wadanda suke ganin kasuwanci da riba duk abu dayane, Allah Ya nuna mana cewa Shi Ya halatta kasuwanci kuma Ya haramta riba, kuma Ya bayyana yalwatur rahmarsa cewa duk wanda wa'azi yazo gareshi ya ji cewa ta'amuli da riba Allah Ya haramta shi kuma ya hanu ya yarda da haramcin ya tuba to abinda ya yi da ya wuce, amma sauran al'amarin sa yana wurin maliccinsa.
Hakanan bayan wadannan ayoyin biyu Allah madaukakin sarki Ya ce ''Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kubar abinda ya saura na riba har in kun kasance ku muminaine. * Har idan baku aikata (Tuba ba) to ana shelanta muku yaki da Allah da Manzanshi, idan kuka tuba kuna da asalin dukiyarku, kada kuyi zalinci ba kuma za'a taba zaluntar ku ba.'' Bakara, aya ta:278-279.
A iya sanina Masu mu'amala da riba da masu kiyayya da salihan bayi sukadai Allah ya shelantawa yaki, lalle wannan kadai ya ishi bala'I ga masu ta'amuli da riba.   
Hakanan kuma Ma'aikin Allah Ya tsoratar akan ma'amala da riba, Jabir dan Abdullah ya ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah ya ce: Ma'aikin Allah Ya tsinewa wanda ya bada riba da wanda akaba, da wanda ya rubuta (sakatare) da wadanda suka tsaya amatsayin shaidu' Ma'aikin Allah Yace ''Duk daya suke'' Muslim ya ruwaito hadisi na 1597, da Ibnu Hajar a Bulughul Marama Hadisi na 801. Hakika wannan tsinuwa da Ma'aikin Allah Ya yi wa masu ta'amali da riba lalle yana muna mana bala'in da ke cikin riba, mutum na farko da aka tsinewa shine wanda ya bayar ko waye talaka ko mai kuli, shugaba ko wanda ake shugabanta. Mutum na biyu shine 'Wanda akaba' ko waye kuwa. Mutum na uku 'Wanda ya zama mai rubutu a tsakanin maikarba da mai bayarwa' mutum na karshe da tsinuwar Ma'aikin Allah ta hada dashi a wannan Hadisin 'Sune wadanda suke shaida' sanna Ma'aikin Allah Ya ce duka daya suke. Allah ya tsaremu baki daya.  
Ita riba tana cikin abubuwan da dukka shari'un da suka gaba ta sun haramtar da ita, asalima shi ta'amuli da riba daya ne daga cikin siffofin yahudawa da Allah Ya tsine musu tsinuwar kuma ta har abada.
Kadan Daga Cikin Abinda Yasa Aka Haramta Riba.
Tabbas akwai cindukiyar mutane ba tare da hakki shar'antattacceba, akwai kuma cutar da talakawa da mabukata ta yadda ake nunnunka musu bashi musammamma idan sun kasa biya, sannan akwai kuma rashin tausayi, sannan al'amarine da yake toshe hanyar bada kyakkyawan taimako, yake bude hanyar mummunan taimako wanda ke dankwafar da marashi ko-da-ko Bankine koma kasa, abune kuma da yake gurgunta kasuwanci da masana'antu, sanna kuma al'amarine da yake zama sanadiyyar salwantar dukiya kuma gashi yadda musulunci ya baiwa dukiya kima da daraja, wannan yasa duk abinda zai kawowa dukiya cikas musulunci ya kawar da shi kamar sata, sane, fashi, daukar dukiya a bada ita ga wanda baida kimiyyar kula da ita d.s, to wannan yana daga cikin abinda yasa aka haramta Riba, idan ba'a manta ba ashekara ta 2009 da duniya ta samu kanta cikin matsin tattalin arziki ai nan-da-nan manyan bankuma a turai suka bayyana cewa sun kudin ruwa da suke karba da kashi kaza (a yanzu na manta) ashe suma sunsan cewa riba tana cikin abinda ke karya tattalin arziki cikin gaggawa.
Kada maikarau ya sha'afa cin Riba yana daya daga cikin siffofin Yahudawa da Allah Madaukakin sarki ya tsine musu a kanta, Allah madaukakin sarki Yana cewa: ''Kuma saboda tsananin zalincin Yahudawa muka haramta musu abubu masu dadi, da kuma yadda suke kange (mutane) masu yawa daga hanyar daidai, da kuma yadda suke karbar kudin Ruwa kuma tuni an hanasu, da kuma yadda suke cin dukiyar mutane da barna''. Suratun Nisa'i, aya ta 161.  
Riba itace kari akan wadansu abubuwa kebantattu,kamar yadda bayani ya gabata, ashe wannan yana nuna mana cewa ba komai bane riba ke shiga cikinshi. To yanzu wadanne abubuwane wadannan?. Ankarbo daga Ubata dan Samit –Allah Ya kara masa yarda- Hadisine Marfu'I yace ''Zinare da Zinare, Azufra da Azurfa, Iburo da Iburo, Shinkafa da Shinkafa, Dabino da Dabino, Gishiri da Gishiri, (ayi su) daidai-wa-daida, Hannu-da-Hannu''. Bukhari Hadisi na 2176 da Muslim 1584 (kuma wannan lafazin riwayar Musline). Ayanzu wannan Hadisi ya zayyano mana abubuwa guda shida ya kuma bayyana mana yadda za'a yi mu'amala da su, yadda za'a yi mu'amala da su sharuddabe guda biyu alokacin da bubuwan suka zama jinsi guda, abu na farko ya zama daidai wa-dai-da, abu na biyu ya zama hannu-da-hannu, idan aka saba haka to an ci Riba kamar yadda wadansu hadisan suka nuna.
Mudauki misalan abubuwa biyu cikin wadancan abubuwa shida da aka anbata a Hadisi, misalin abu na farko shine 'Zinare' idan kana da zinare nima ina da zinare ina son inbaka nawa in karbi naka (misanye) sai aka auna nauyinsu ya zama daidai to anan sai inkarbi naka ka karbi nawa (hannun-kuturu-da-na-makaho) ba zan kara maka komaiba, ba zaka karamin komai ba, in an yi kari to wannan Karin ya zama riba, ko da an gyara na wani ba'a gyara na wani ba, balle na ki dankunnen zinarine nawa kuma awarwarone duk ba wani kari, kenan idan kai da kake sayarwa na kawo maka nawa kilo ashirin na awarwaro sai kaban kilo ashirin na sarka, shikenan taro ya tashi ba maganar in kara maka dari biyar ko dubu, in an yi kari to an ci riba.
Misalin abu na biyu kuwa shine mudauki shinkafa, Shinkafa bakidayanta jinsi gudace ta gida da ta waje, kenan yanzu idan na baka shinfa 'yar gwamnati kwano goma kai kuma kana da ta gida to kaima kwano goma zaka bani hannu-da-hannu, idan aka yi kari to an ci riba, ashe yanzu idan aka baka shinkafar gwamnati kwano goma aka ce ka bada ta gida kwano goma da rabi to wannan abinda aka kara ya zama riba komai kankantar shi hakanan komai girmanshi, Allah Ya sawwake, lalle wannan yana nuna mana mu kusanci malamai kenan, hakanan idan aka bayar da ta gwamnati yanzu kwano goma sai aka ce kazo bayan karfe kaza ka karbi ta gida kwano goman shima ya zama riba tunda an sami jinkiri, domin hadisin ya nuna ayi daidai-wa-daida, kuma hannu da hannu, kamar yadda bayani zaizo, da izinin Allah.
Mu koma kan wancan Hadisin da ya lissafafa abubuwa shida, sai malamai magabata sukece 'Haramcin riba bai takaitu a kan wadannacan abubuwa shida kadai ba, a'a, sudai wadancan shida sune asali duk abinda ke da alaka da daya daga cikinsu sai yakarbi hukuncinshi. Sai malaman sukace abinda yasa Zinariya da Azurfa (wato biyun farko a Hadisin) suka zama abinda riba ta ke shiga shine don suna kudi, saboda haka duk abinda yake kudine Nairace ko Riyal ko Dala, ko Saifa koma nenene indai kune to shima hukuncin Zinariya da Azurfa ya hau kan shi, wannan zai nuna maka gamewa ta musulunci da kuma Mu'ujizar Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ta yadda ya yi jawabin da ya shafi Riyal da Dala da Naira wanda yake alokacin da yake wannan jawabi babu wadannan kudade, Allah Ya kara masa daukaka, amin.
      Canjin-kudi: Canjin-kudi nau'ine na kasuwanci da Allah ya halattashi, akan hakane har ake da 'yan-canji da shugaban canji. Sai dai mu sani kudin da ake canzawa sun kasu kashi biyu, akwai wadanda suke jinsi guda, kamar Naira da Naira ko Riyal da Riyal ko Dala da Dala d.s, to dukkan kudadan da suke a junansu jinsi guda suke ya zama wajibi wurin yin canji asan an cika sharudda guda biyu:
(a)    Hannnu-da-hannu: idan aka sami jinkiri to anci riba, misali idan na zo ka canzamin N500, to bai halatta ka karba kace indawo anjima in karbi canjinba.
(b)    Daidaiwadaida: kenan bai halatta in baka N500ba, kai kuma ka bani N490 ko don sabbine ko dai wadansu al'amura.
 Sai kuma kudaden da jinsinsu ba guda ba ne, kamar Naira da Dala ko Saifa da Riya, anan ya halatta asami fifiko inbaka Dala 100 ka bani N150,000. amma dole ya zama hannu da hannu, bai halatta a sami jinkiriba.
 Abinci: Musanyar abinci da abinci hasne kuma nau'ine na halastaccan kasuwanci, saidai shima ya kamata asan abinda suke jinsi guda da kuma wanda suke ba jinsi gudaba. Kamar shinkafa baki dayanta jinsi gudane, kenan lokacin musanye dole asamu sharudda biyu hannu da hannu kuma daidai wadaida, kamar yadda bayani ya gabata, hakanamma gero da gero bai halatta inbaka gero na bara kwano goma kai kuma ka bani na bana kwano tara ko shadayaba.
       Lalle wannan yana nuna mana yadda kofofin afkawa riba suke da yawa domin sau da yawa wani yana bada bashin kudi akan idan za'a dawo mishi da su sai anyi kari, wanda yake da yawan Bankuna da daidaikun jama'a akan haka suka ginu. Wannan nau'uka na riba bayanansu ba zai wadatarba a dan wannan rubutu, sai dai a kusanci malamai sannan kuma alizimci karatu akan kasuwanci, domin hatsarin da yake cikin Riba da fushin Allah akan dukkan mai ta'amuli da ita hard a wanda ya rubuta da wanda ya tsaya shaida duk tsinuwar Allah ta hau kansu kamar yadda bayani ya gabata, Allah muna rokonka ka ciyarmu abinda yake halal kuma ka sa mu cika da imani, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
 Minna, jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
: munbarin musulunci

Sunday, October 14, 2012

HUKUNCE-HUKUNCEN SALLAR IDI


Gabatarwa: Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na SALLAR IDI! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abinda ya rage kawai a garemu shi ne bi, komai angama, Allah tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin Ma'aikin Allah.
Mecece Sallar Idi: ''Ita sallar idi sallace da ake gabatar da ita a wani lokaci kebantacce, awata siffa kebantacciya, sau biyu a shekara''. Kafin mu kai ga fashin bakin wannan ta'arifi na sallar idi, bari mu gabatar da tabbatuwarta tukunna.
Tabbatuwar Sallar Idi: Sallolin idi guda biyu da musulunci yake da su (Karamar Sallah da Babbar Sallah) kowacce ta tabbata a shara'a, ba wai bikine haka kwai na gargajiyaba.
Tabbatuwar Karamar Sallah: itace sallar da ake gabatarwa a ranar 1 ga Shawwal, don godiya ga Allah akan baiwar da ya yi mana na kammala azumin watan Ramadan, wannan sallar ta tabbata a Suratul-A'alah aya ta:14-15, Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Tabbas duk wanda ya bayar da zakka (Fidda-kai) ya rabauta. Kuma ya anbaci sunan UbangijinSa sannan kuma ya yi sallah''. Sai malamai sukace 'Zakka da aka anbata a ayar farko itace zakkar fidda-kai, Sallah kuma da aka anbata a aya ta biyu itace, karamar sallah domin itace ake fitar da zakkar Fidda-kai kafin a ta fi, sannan kuma ga zikirin da aka an'anbata shine wanda ake yi lokacin tafiya sallar idin'.
Tabbatuwar Babbar Sallah: Ita kuma sallah ce da ake gabatar da ita a ranar 10 ga watan Zul-Hajji. Ita ma babbar Sallah ta tabbata a Suratul-Kauthar a aya ta: 2. a inda Allah madaukakin sarki yake cewa ''Ka yi Sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke (abin hadayarka)'', malamai sukace 'Babbar Sallah ce domin an hada Sallah da Yanka' a ayar kamar wacce ta gabata an'hada Zakka da Sallah. Wannan tabbatuwar  wadannan sallolike nan ta ayoyin alkur'ani, hakanamma sun tabbata ta ayyukan Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, Bukhari da Muslim da Abu-Daud da Nasa'i duk sun ruwaito daga Jabir-Allah Ya kara masa yarda yace ''Na harci Sallar idi tare da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- sai ya fara gabatar da sallah kafin Huduba ba tare da an yi kiran sallaba ko an tada Ikama''. Haka shima Bara'u dan Azib –Allah Ya kara masa yarda yace ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya yi mana huduba a ranar babbar sallah, bayan ya idar da sallah sai yace ''Duk wanda ya yi wannan sallar tamu, kuma ya yi yanka irin namu to yankanshi ya yi daidai, wandako ya yanka kafin ayi sallah to wannan bashi (da ladan) yanka''. Wannan hadisin malaman Hadisi bakwaine suka ruwaito shi.
Hukuncin Sallar Idi: Hukuncin sallar idi shine, Sunnace mai karfin gaske, domin Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya aikata ta kuma ya lizimceta, hakanan kuma ya fitar da mata da kanan yara zuwa halartar wannan sallah. Saboda haka bai kamata mutum ya yi sakaci da itaba har ya rasa samun wannan sallah wanda saboda ita nema aka bada hutu a kasa baki daya, ka rufe shagonka na kasuwanci ka dakatar da ayyukanka.
Lokacin Sallar Idi: Kamar yadda bayani ya gabata a ta'arifi cewa sallace da ake gabatarwa a lokaci kebantacce to wannan lokacin kuwa shine ''Daga lokacin da rana ta fito ta daga kamar tsawon sandar mashi harzuwa lokacin da rana zata karkata daga tsakiyar sama''. Amma malamai sukace 'An fi so a babbar sallah a yi ta da wurwuri domin mutane su samu su koma gida domin su yanka layyarsu a daidai lokacin walaha, sannan kuma su ci abinci domin basu ci ba suka fito sallah. Amma akaramar sallah an fi so a dan jinkirta sallar domin mutane su samu su gama fitar da Zakkar su ta fidda-kai, su kuma ci abinci domin iti an fi so a ci kafin a fito sallah'.
Ladubban Sallar Idi: Akwai wadansu ladubba da yakamata a ladabtu da su, wadannan ladubba suna da yawa daga ciki akwai:
1.       Yin wanka da sanya turare da kuma sanya tufafi masu kyau sababbine ko nada.
2.       Hakanan yana daga cikin labudda a ci abinci kafin a fita sallar idi a karamar sallah, da kuma jinkirta cin abinci a babbar sallah har sai an yi sallah, da kuma cin wani abu na hantar dabbar layyah ga wanda ya yi. Ankarbo daga Buraidah –Allah Ya yarda da shi- yace; ''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya kasance baya fita zuwa masallcin idi a karamar sallah har sai ya ci abinci, kuma ya kasance baya cin abinci a babbar sallah har sai ya dawo daga masallacin idi, sai ya ci wani abu na dabbar layyarsa''.wannan Hadisi Tirmizine ya ruwaito.
3.        Kana yana daga cikin ladubba yin kabarbari, kuma lafazinta shine: Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil Hamd.
4.       Yin gaisuwar sallah wato kacewa dan'uwanka musulmi ''Allah Ya karba mana ya karba muku''.
Siffar Sallar Idi: Kamar yadda ya gabata a farkon bayani cewa sallace da ake gabatar da ita a wata siffa kebantatta, wannan siffa kuwa itace; wannan sallah ana yin ta ne Raka'a biyu, kuma ana bayyana karatun, ba tare da angabatar da kiran sallah ba, ko tada ikama, sannan kuma ba'a gabatar da nafila kafin sallar ko bayan sallar. A raka'ar farko bayan kabbarar harama anayin kabarbari shida kafin fara karatu (wato kabarbari bakwai kenana). A Raka'a ta biyu bayan kabbarar tasowa sai a yi kabarbari biyar, kafin fara karatu (wato kabarbari shida kenan), wadannan kabarbari liman da mamu duk suna yinsu sai dai mamu baya karatun sallah saboda karatun liman, sannan sai ayi sallar kamar sauran salloli, bayan liman ya yi Tahiya ya yi sallama sai ya gabatar da Huduba, sannan yana da matukar muhimmanci a tsaya a saurari hudubar, wadannanfa sune ayyukan ranar, amma wacce gaggawa mutane suke yi suke barin sauraron Hudubar?.
Wanda bai samu sallar idi ba ya samu ya yi sallah Raka'a hudu kamar nafilfili, idan kuma ya ga dama ya yi ta a siffar sallar idi.
Idan kazo ka sami liman yana Tahiya sai ka zauna tare da shi, idan ya yi sallama sai ka mike ka kawo raka'oinka biyu a siffar su da ta gabata.
Wadansu Mas'aloli: A yanzu za'a kawo wadansu halaye da mutum yakan samu kanshi a ciki idan ya zo ya samu tuni anfara sallah.
1.      Idan mutum ya zo ya sami liman ya kammala kabarbari ya fara karatu ya zai yi?. Amsa: Anan zaka yi wadannan kabarbarin, kasancewar ba abune mejan lokaci ba, sannan sai ka raurari karatun liman.
2.       Idan ka zo ka sami liman ya fara kabarbari amma bai gamaba, to anan zaka yi sauran kabarbarin da suka ragewa liman tare da shi, sannan sai ka kawo wadanda suka wuceka, koda liman ya fara karatu, kenan anan ba zaka yi wadanda suka wucekaba a lokacin kabarbarin liman.
3.      Idan kazo ka sami liman yana Ruku'u sai ka yi kabbarar harama kadai ka bishi, ba sai ka kawo sauran kabarbarinba.
Tambihi: Ya kamata mu san girman wadannan salloli da matsayinsu a addini, tunda har yakai Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa a fita sallar har da mata da kananan yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da wurin sallah idan anzo huduba suma sai su anfana. Kada mu sha'afa akan wannan sallarne aka bada hutu duka kasa, aka rufe shaguna kada mutum ya shagala a wannan lokaci da abinda zai hana mishi samun wannan sallah. Sannan kuma a kula da yara da irin suturar da za su sa, domin idan ka ga wadansu yaran ba kace 'ya'yan musulmi bane, wannan baidace ba kuma baikamata, wasu kuma rawa kamar mazari, Allah Ya sawwaka, amin.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata ya bayyana a garemu cewar sallar idi ba wata gargajiya bace ibadace da Allah ya shar'anta ta ta harshen fiyayyan halitta Annabi Muhammad –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, itako ibada anayinta akan yadda aka tsarata ne, Allah ya karbi ibadarmu ya sa ayi sallah lamilafiya ya tsaremu ya tsare mana imaninnu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad Sadisu

Wednesday, October 3, 2012

Aikin Hajji A Wannan Shekarar 1433 (2012) Ina Mafita??


Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga ma'aikin Allah. Bayan haka lalle wannan masifa da ta aukawa kasarnan a wannan gagarumin aiki wanda yake rukunine daga cikin rukunan addinin musulunci abin a tsaya ai nazarinta ne domin aga ta ina ta fito kuma ya za'a tunkareta ta yadda ba zata sake aukuwaba, domin ace mutum ya isa kasa mai tsarki lamilafiya amma kuma a dawo da shi kai wannan ba karamin tashin hankali bane Ya Allah muna rokonka da kada musake ganin maimaituwar wannan al'amari. Kamar yadda na fada lalle ya kamata mu tsaya mu yi wa wannan lamari karatun ta-natsu, mabudin wannan karatu itace ayar dake cikin Suratus Shura aya ta 30. ''Kuma duk abinda ya sameku na kowacce irin masifa to fa saboda abinda kuka gabatarne, kuma (Allah) Yana ga abubuwa masu tarin yawa''.
          Lalle la'akari da wannan ayar yana dakyau mu tsaya muga me aka gabatar da ya haifar da wannan al'amari don asan matakin da za'a dauka don hana aukuwar irinshi nan gaba. Ni a ganina wadannan al'amurra sune kamar haka:
1. Mahrami: Shine mutumin da yake haramunne ya auri matar da yake tare da ita (kamar uba mahramine na 'yarshi, ko kaka ko siriki) shi yasa sai ace mahrami ko miji, Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa: Bai halatta ga dukkan matar da tai imani da Allah da ranar lahira da ta yi tafiya kwana guda ba tare da maharraminta ba'' Hadisai da suka zo daga ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- a kan haka suna da matukar yawa da fayyace al'amurra a fili da suke nuna irin gatan da musulunci ya yi mace lura da cewa ita mai raunice baibukar taimakoce a koda yaushe  kuma ko wanne iri. An ruwaito cewa wani daga cikin Sahabban ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- an sanyashi cikin wadanda za su tafi yaki sai yace medakinshi zata tafi aikin hajji sai ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yace acire sunansa ya tafi ya je ya yi aikin hajji tare da maidakinshi. Kuma wannan al'amarii sannannene cewa alokacin da mace take tare da mahraminta ko mijinta zata dada kamewa doruwa akan wacce take da ita, in kuma ba kamammiya bace to zata kame da izinin Allah, kuma zata zama tana da abokin hira a wannan tafiyar, hikimomi da zaka iya zakulowa cikin muhimmacin mahrami a tare da mace a Halin tafiya ba karamin al'amari bane, duk wanda ya taba yin aikin Hajji zai tabbatar da muhimmancin mahrami tare da mace, ba Mijin-Biza ba domin akwai halin da ake shiga na sai ka rike mata hannu ko jiki, wanda yake haka ba zai yiwuba idan ba maharramaka bace. Malamai sun karawa juna sani kan abinda ya shafi aikin Hajji shin idan aka sami tawaga amintacciya  mace zata iya tafiya a cikinsu ko dab a mahraminta? Sai wannan tawaga ta zama kamar mataimaka a gareta? Malamai da yawa sun tafi akan haka,
          Maganar mahrami maganace da ta taso a aikin Hajjin wannan shekarar ta 1433 Hijira ko 2012 miladiyya, a inda akan hakanne hukumar kasar Saudiya ta dawo da mahajjata mata masu tarin yawa daga kasar, na farko da maganar mahrami tabbatacciiyace a shara'a domin ta fitone daga bakin Ma'aikin Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ba Magana bace da hukumar kasar Saudiya ta kirkiri bam domin na ji Nura Das Ahirarsa da jaridar Leadership Hausa bugu na 313, a shafi na 25 yana cewa Ba kowanne mahajjaci bane ke bin akidar Wahabiyaci, Su a mazahabinsu na Ja'afariyyah wanda aka fi sani Shi'a mace idan ta amincewa kanta ko waliyyanta sun amince mata zata iya tafiya ko inane, wannan Magana tasu ta nuna abinda acewa su Shi'a ba abinda ya hada su da karantarwar ma'aikin Allah, in banda ina maganar bin tafarkin ma'aikin Allah ina kuma maganar wahabiyanci?. Maganar maharami manace data mamaye kafafan yada rabaru a kasarnan kuma maganace da take bukatar a tsaya a yi mata karatun-ta-tsau domin sanin hikimomi da tausayawa da musulunci ya yiwa 'ya mace, kafafan yada labaru sun cancanci yabo yadda suka tunubi malumma akan wannan al'amari wato suka maida al'amarin zuwa ga masu shi. To amma hanzari-ba-gudu-ba maganar da kafofin yada labarai suke yi na cewa anya maganar mahramce kadai tasa wannan al'amari ya faru koko akwai lauje cikin nadi domin mata 'yan Nijeriya kawai aka dawo da su banda 'yan wadansu kasashen? Wannan maganar ya kamata a yi la'akari da ita, wannan ya kaimu abu na biiyu wato.
2. Gurbacewar Tarbiya: A gaskiya Najeriya tana da matukar kima da daraja a idanun kasar Saudiya, amma a gaskiya halayyar da 'yan Najeriya suke nunawa a wadannan wurare masu tsarki musamman ma a birnin Makkah birni mafi tsarki da daraja gaskiya a kwai bantakaici, mata nawane suka tsallake mazajensu su kai zaman dirshan a birnin makkah, me ya kaita? me take yi? Asalin Magana a musulunci mace bata ciyar da kanta kwata-kwata, idan ta yi aure mijinta ya ciyar da ita idan batai aure ba mahaifinta ko waliyyinta ya ciyar da ita. Duk mutumin da ya tabayin aikin hajji zai ga irin halayya da sutura ta rashin mutunci da wasu matan -wasu cikin mahajjata- suke nunawa a ranar sallah matsattsun kaya wasanni marasa kyau tun kafin a gama zaman mina, ballantana a gidan da alhazai suka sauka ka ga yadda ake da 'yan-tuwo-tuwodin abin zai baka mamaki kamar ba a kasa mai tsarki ake ba, idan akai maganar dogon-gida ko Sara-Mansur abirni Makkah da sauran unguwanni kamar su Jabal abin ba'a cewa komai. Ni inagani ya kamata ofishi Najeriya ya shirya wata bita da karantar da 'yan Najeriya da tarbiyantar da su a biranan Makkah da Jiddah da kuma Madina, kuma ya tashi tsaye yaga 'yan Najeriya suna zaune akasar a bisa doka, anan ba ina cewa duka 'yan Najeriya haka suke ba a'a kwata-kwata, akwai tsayayyu, amma mu sani idan fitina ta zo ba tana takaituwa bane ga wadanda suka janyota kamar yadda muka gani a wannan shekarar, zaka iya samun macan da bata ganin jirgin sama a kasaba sai wannan karon amma gashi bala'in wasu ya janyo mata, Allah Madaukakin sarki yana cewa:
          ''Kuma ku ji tsoron fitina wacce ba ta samun danda suka yi zalunci daga cikinku kadai, kuma ku sani lalle ne Allah Mai tsanani ukuba ne'' Sutul-Anfalm aya ta 25.
Mai karatu idan kana jin abinda 'yan Najeriya suke aikata a kasa mai tsarki musamman mata abin zai dauure maka kai matuka da gaske, yanzu idan aka ce maka dukkan matan da suka je Umarar nan data wuce sun dawo nan Najeriya? Me zakace ko kuma ka tambaya.
          Sannan suma hukumar alhazai ta Najeriya ya kamata ta tashi haikan wurin sanyawa maniyyata tsoron Allah da kula da dokokin Sa, a samu malamai masu tsoron Allah wadanda ba himmarsu a biya musu kujeraba, wadannan dakakkun malamai sukasance na dindin-din ko kaso mai yawa daga cikin su sannan abasu damar gudanar da aikin nasu.
3. Mace mai Juna-biyu: Lallekan akwai maganar wahala ga mace mai juna-biyu a aikin hajji mutum ma yana shi kadai ya yacika, amma irin matakin da hukuma ta dauka na haramtawa mace mai juna-biyu aikin hajji wai koda kuwa na wata dayane gaskiya ya kamata a sake duba wannan Magana idan andubeta ta bangaren kiwon lafiya a dubeta ta bangaren addini, babu wani dalili aduk abinda malamai sukai ijima'i aka kafa dalili da shi da ya nuna cewa mace mai juna-biyu bata da damar zuwa aikin hajji, ni ina jin tsoro kada irin wannan hani da aka yiwa wadannan matan yasa aka wannan dayyar matsalar, kada mu sha'afa maganar addini ake yi asalima shi aikin hajjin ginshikine daga cikin shika-shikan musulunci guda biyar, saboda haka kada ka kuskura ka hana wani wannan aiki ba tare da kanada kakkarfan dalili da zaka gabatarwa Allah ba a ranar kiyama, a shekarar da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- Ya yi aikin Hajji wanda shine kuma akekira da hajjin bankwana, adaidai lokacin da Ma'aikin Allah ya isa Zul-Hulaifah inda nan ne mikatin mutanan madina yana zuwa wurin medakin Sayyidina Abubakar ta sauka (tahaihu), kaga kenan ta fito ne ma da tsohon ciki, awannan tafiya da ake akasa ko a doki ko a rakumi, wanda ba za'a hada hakan da jirgin-sama ba ko na ruwa ko mota ba. Wannan matsananciyar dokar data zamar da mata da yawa Hajji Haram ya kamata a sake dubata, wadda ta sanadiyyar ta ake ruwaito mata da yawa suna zubar da cikinsu, irin wannan mataki na anfani da na'urori masu gani harhanji masu ganin-kwakwaf na cewar indai har anbankado cewar tana da ciki to Hajji Haram ya kamata a sake dubawa.
Shawarwari/Mafita: Ni ina ganin bin wadannan shawarwari zai zama wata mafita ga rashin sake maimaituwar irin wannan al'amari, da muke rokon Allah Ya kiyayemu daga maimaituwar wannan alamari:
1.     Tsayawa da tabbatar da mahrami shar'antacce muddin akwai yadda za'a same shi  ba abinda ake cewa mijin-biza ba.
2.     Gabatar da cikakkiyar bita akan mece ''Rifka Ma'amuna'' sannan suwaye, a kuma gabatar musu da bita ta sanin makamar aikin ''Rifka Ma'amuna''.
3.     Tashi tsaye domin a wayar da kan mutane dangane da matsayin mahrami a shara'a, da kuma bayanin gatan da musulunci ya yiwa mata akan sanya musu mahrami da ya yi.
4.     Kimsawa maniyyata tsoron Allah madaukakin sarki, da kuma falalar da maibin Allah yake da ita da kuma narkon sabawa Allah, a gida Najeriya ko a kasa mai tsarki.
5.     Kimsawa maniyyata bin tafarkin Ma'aikin Allah da kuma cewar rabauta duniya da lahira ta tattarune akan tsantsanta biyayya ga reshi.
6.     Karfa halartar maniyyata  wuraran bita.
7.     Samar da wata manhaja ta baidaya kakkarfa akan abinda ya sha fi bita.
8.     Kara samarwa malamai masu tsoron Allah gurabu a harkar hajji, da kuma basu karfin fada aji.
9.     Kara sa ido da dokar da ta dace ga duk wanda ya yi fitsara a duk wurin da ya shafi Hajji tun daga wuraren bita har kamala aikin hajji.
10. Sanya ido ga dukkanin jahar da ta bari wani alhajinta ya ki dawowa.
11. Karamin ofishin jakadancin Najeriya dake birinin Jiddah ya samara da wata ganawa da 'yan Najeriya dake Makkah, Jiddah da Madina domin karantar da su da kuma kara nuna musu tsarkin wurin da suke zaune.
12. Daukar matakin ladabtarwa ga duk dan Najeriyar da ya karya ittifakiyar da aka yi da kasar Saudiyyah.
13. Sake duba maganar mace me juna-biyu, domin kada mu manta tun kafin Saudiya su nemi su zamar da wasu mata Hajji Haram tuni Najeriya ta zamar da wasu.

          Allah madaukakin sarki ya tsaremu ya tsare mana imanimmu, ya kawo mana karshen wannan kiki-kaka da ake yi da alheri, Allah ya kai alhazammu mata da maza kasa mai tsarki lafiya ya kuma dawo mana da su lafiya. Ya Allah katsare mana kasarmu ka zaunar da mu lafiya da dukkanin kasashen musulmi bakiya, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
 e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad Sadisu