Gabatarwa: Dasunan Allah Mai
yawan rahama maiyawan jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan
halittar Allah Annabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi
baki daya. Bayan haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare
da ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi ne na SALLAR
IDI! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana komai abinda ya rage kawai a
garemu shi ne bi, komai angama, Allah tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin
Ma'aikin Allah.
Mecece Sallar Idi: ''Ita sallar
idi sallace da ake gabatar da ita a wani lokaci kebantacce, awata siffa
kebantacciya, sau biyu a shekara''. Kafin mu kai ga fashin bakin wannan
ta'arifi na sallar idi, bari mu gabatar da tabbatuwarta tukunna.
Tabbatuwar Sallar
Idi:
Sallolin idi guda biyu da musulunci yake da su (Karamar Sallah da Babbar
Sallah) kowacce ta tabbata a shara'a, ba wai bikine haka kwai na gargajiyaba.
Tabbatuwar Karamar
Sallah: itace sallar da ake gabatarwa a ranar 1 ga Shawwal, don
godiya ga Allah akan baiwar da ya yi mana na kammala azumin watan Ramadan,
wannan sallar ta tabbata a Suratul-A'alah aya ta:14-15, Allah madaukakin sarki
yana cewa: ''Tabbas duk wanda ya bayar da zakka (Fidda-kai) ya rabauta.
Kuma ya anbaci sunan UbangijinSa sannan kuma ya yi sallah''. Sai
malamai sukace 'Zakka da aka anbata a ayar farko itace zakkar fidda-kai,
Sallah kuma da aka anbata a aya ta biyu itace, karamar sallah domin itace ake
fitar da zakkar Fidda-kai kafin a ta fi, sannan kuma ga zikirin da aka
an'anbata shine wanda ake yi lokacin tafiya sallar idin'.
Tabbatuwar Babbar
Sallah: Ita kuma sallah ce da ake gabatar da ita a ranar 10 ga watan Zul-Hajji.
Ita ma babbar Sallah ta tabbata a Suratul-Kauthar a aya ta: 2. a inda Allah
madaukakin sarki yake cewa ''Ka yi Sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke
(abin hadayarka)'', malamai sukace 'Babbar Sallah ce domin an hada
Sallah da Yanka' a ayar kamar wacce ta gabata an'hada Zakka da Sallah. Wannan
tabbatuwar wadannan sallolike nan ta
ayoyin alkur'ani, hakanamma sun tabbata ta ayyukan Ma'aikin Allah –Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi-, Bukhari da Muslim da Abu-Daud da Nasa'i
duk sun ruwaito daga Jabir-Allah Ya kara masa yarda yace ''Na harci
Sallar idi tare da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-
sai ya fara gabatar da sallah kafin Huduba ba tare da an yi kiran sallaba ko an
tada Ikama''. Haka shima Bara'u dan Azib –Allah Ya kara masa yarda yace
''Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya yi mana
huduba a ranar babbar sallah, bayan ya idar da sallah sai yace ''Duk wanda ya
yi wannan sallar tamu, kuma ya yi yanka irin namu to yankanshi ya yi daidai,
wandako ya yanka kafin ayi sallah to wannan bashi (da ladan) yanka''.
Wannan hadisin malaman Hadisi bakwaine suka ruwaito shi.
Hukuncin Sallar
Idi:
Hukuncin sallar idi shine, Sunnace mai karfin gaske, domin Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya aikata ta kuma ya lizimceta,
hakanan kuma ya fitar da mata da kanan yara zuwa halartar wannan sallah. Saboda
haka bai kamata mutum ya yi sakaci da itaba har ya rasa samun wannan sallah
wanda saboda ita nema aka bada hutu a kasa baki daya, ka rufe shagonka na
kasuwanci ka dakatar da ayyukanka.
Lokacin Sallar Idi: Kamar yadda bayani
ya gabata a ta'arifi cewa sallace da ake gabatarwa a lokaci kebantacce to
wannan lokacin kuwa shine ''Daga lokacin da rana ta fito ta daga kamar
tsawon sandar mashi harzuwa lokacin da rana zata karkata daga tsakiyar sama''.
Amma malamai sukace 'An fi so a babbar sallah a yi ta da wurwuri domin
mutane su samu su koma gida domin su yanka layyarsu a daidai lokacin walaha,
sannan kuma su ci abinci domin basu ci ba suka fito sallah. Amma akaramar
sallah an fi so a dan jinkirta sallar domin mutane su samu su gama fitar da
Zakkar su ta fidda-kai, su kuma ci abinci domin iti an fi so a ci kafin a fito
sallah'.
Ladubban Sallar
Idi:
Akwai wadansu ladubba da yakamata a ladabtu da su, wadannan ladubba suna da
yawa daga ciki akwai:
1.
Yin wanka da sanya turare da kuma sanya
tufafi masu kyau sababbine ko nada.
2.
Hakanan yana daga cikin labudda a ci abinci
kafin a fita sallar idi a karamar sallah, da kuma jinkirta cin abinci a babbar
sallah har sai an yi sallah, da kuma cin wani abu na hantar dabbar layyah ga
wanda ya yi. Ankarbo daga Buraidah –Allah Ya yarda da shi- yace; ''Ma'aikin
Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya kasance baya fita zuwa
masallcin idi a karamar sallah har sai ya ci abinci, kuma ya kasance baya cin
abinci a babbar sallah har sai ya dawo daga masallacin idi, sai ya ci wani abu
na dabbar layyarsa''.wannan Hadisi Tirmizine ya ruwaito.
3.
Kana
yana daga cikin ladubba yin kabarbari, kuma lafazinta shine: Allahu
Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Walillahil
Hamd.
4.
Yin gaisuwar sallah wato kacewa dan'uwanka
musulmi ''Allah Ya karba mana ya karba muku''.
Siffar Sallar Idi: Kamar yadda ya
gabata a farkon bayani cewa sallace da ake gabatar da ita a wata siffa
kebantatta, wannan siffa kuwa itace; wannan sallah ana yin ta ne Raka'a biyu,
kuma ana bayyana karatun, ba tare da angabatar da kiran sallah ba, ko tada
ikama, sannan kuma ba'a gabatar da nafila kafin sallar ko bayan sallar. A
raka'ar farko bayan kabbarar harama anayin kabarbari shida kafin fara karatu
(wato kabarbari bakwai kenana). A Raka'a ta biyu bayan kabbarar tasowa sai a yi
kabarbari biyar, kafin fara karatu (wato kabarbari shida kenan), wadannan
kabarbari liman da mamu duk suna yinsu sai dai mamu baya karatun sallah saboda
karatun liman, sannan sai ayi sallar kamar sauran salloli, bayan liman ya yi
Tahiya ya yi sallama sai ya gabatar da Huduba, sannan yana da matukar
muhimmanci a tsaya a saurari hudubar, wadannanfa sune ayyukan ranar, amma wacce
gaggawa mutane suke yi suke barin sauraron Hudubar?.
Wanda bai samu
sallar idi ba ya samu ya yi sallah Raka'a hudu kamar nafilfili, idan kuma ya ga
dama ya yi ta a siffar sallar idi.
Idan kazo ka sami
liman yana Tahiya sai ka zauna tare da shi, idan ya yi sallama sai ka mike ka
kawo raka'oinka biyu a siffar su da ta gabata.
Wadansu Mas'aloli: A yanzu za'a kawo
wadansu halaye da mutum yakan samu kanshi a ciki idan ya zo ya samu tuni anfara
sallah.
1.
Idan mutum ya zo ya sami liman ya kammala
kabarbari ya fara karatu ya zai yi?. Amsa: Anan zaka yi wadannan
kabarbarin, kasancewar ba abune mejan lokaci ba, sannan sai ka raurari karatun
liman.
2.
Idan
ka zo ka sami liman ya fara kabarbari amma bai gamaba, to anan zaka yi sauran
kabarbarin da suka ragewa liman tare da shi, sannan sai ka kawo wadanda suka
wuceka, koda liman ya fara karatu, kenan anan ba zaka yi wadanda suka wucekaba
a lokacin kabarbarin liman.
3.
Idan kazo ka sami liman yana Ruku'u sai ka
yi kabbarar harama kadai ka bishi, ba sai ka kawo sauran kabarbarinba.
Tambihi: Ya kamata mu san
girman wadannan salloli da matsayinsu a addini, tunda har yakai Ma'aikin Allah
–Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- yana cewa a fita sallar har da
mata da kananan yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da
wurin sallah idan anzo huduba suma sai su anfana. Kada mu sha'afa akan wannan
sallarne aka bada hutu duka kasa, aka rufe shaguna kada mutum ya shagala a
wannan lokaci da abinda zai hana mishi samun wannan sallah. Sannan kuma a kula
da yara da irin suturar da za su sa, domin idan ka ga wadansu yaran ba kace
'ya'yan musulmi bane, wannan baidace ba kuma baikamata, wasu kuma rawa kamar
mazari, Allah Ya sawwaka, amin.
Kammalawa: Daga wadannan
bayanai da suka gabata ya bayyana a garemu cewar sallar idi ba wata gargajiya
bace ibadace da Allah ya shar'anta ta ta harshen fiyayyan halitta Annabi
Muhammad –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi-, itako ibada anayinta
akan yadda aka tsarata ne, Allah ya karbi ibadarmu ya sa ayi sallah lamilafiya
ya tsaremu ya tsare mana imaninnu, amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Kwakungu,
bayan Ofishin 'Yansanda,
Minna jahar
Neja Nijeriya.
Za'a iya
tuntuba a.
G.S.M. (+234)8064022965.
e- Imei : aliyusadis@gmail.com
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
www.fecebook.com/Aliyu Muhammad
Sadisu
www.youtube.com/Aliyu Muhammad
Sadisu