SAHUR DA BUDA-BAKI
Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan
jinkai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki
daya. Bayan haka:
A daidai
wannan lokacin da muke kawo bayanai akan hukunce hukuncen azumin watan Ramadan,
to a wannan muna son mu kawo bayanai akan abinda ya shafi hukunce hukuncen
sahur da mude baki, da fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma datar da mu ya kuma
anfanar da mu.
SUHUR.
Shi ne abin ci ko abin sha da mai azumi
yake kusa da fitowar alfijr na biyu. Lokacin kuma shi ake kira da lokacin
suhur.
Kenan anan duk abinda mai azumi ya ci ko
ya sha a daidai wannan lokaci shi ake cewa suhur.
FALALAR SUHUR.
Suhur yana da matukar falala da albarka, Ma’aikin
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
((تسحروا فإن في السحور بركة)). رواه البخاري ومسلم.
Ma’ana: “Ku yi suhur domin a cikin suhur akwai
albarka”. Bukhari da Muslim suka ruwaito.
Wannan na nuna matsayi da daraja kana da
falala ta suhur, ba gwaninta ba ce ko birgewa mutum ya ce ai shi ba ya sahur,
lalle mutum Musulmi ya yi iya kokarinsa wurin cin sahur a kowanne azumi na
farilla ko na nafila, koda ruwa ne ya sha.
LOKACIN CIN SAHUR.
Ana cin suhur ne akarshen dare ba’a
farkon dare ba, ba kuma a tsakiyar dareba, domin kada mutum ya ci abin ci a
farkon dare ko a tsakiyar dare ya ce ya ci suhur, wannan dai ya ci abin ci amma
ba sahur ba.
Kowacce kasa da kuma birane kana da
karkara akwai lokacin da alfijir yake fitowa, domin babu wani takamamman lokaci
na karfe nawa alfijr yake fitowa.
Babban abinda ake so a sani shi ne, alfijir ya
kasu kashi biyu:
Kashi Na Farko: Wanda yake fitowa bada dadewa ba kuma
yake bacewa, to wannan ba ya hana cin abincin suhur, kuma ba ya sawa a yi
sallar asuba.
Kashi Na Biyu: Wanda shi ne yake fitowa ya tokare
sasannin sama, to wannan shi ke hana mai sahur cin abin ci, kuma shi ke sawa a
yi sallar asuba.
FADAKARWA.
Ba’a bukatar mai azumi ya kure lokacin
cin sahur, ana bukatar barin tazara mai dan dama, kamar kuma yadda ba’a bukatar
mutum ya ci shi can cikin dare.
ASSALATU.
Wadansu masallatan suna kiran ASSALATU
a kiran farko, wasu kuma suna kiranta ne a kira na biyu. Babban abin da ake so
agane anan shi ne, masallacin kusa da kai a yaushe ne suke kiran ASSALATU
? a kiran farko ne ko a kira na biyu ?.
Shi lafazin ASSALATU ba
fadin shi ne yake sa wa adaina cin abin ci ba, fitowar alfijir ita take tasa a
daina cin abin ci, saboda haka sai ka tsaya ka natsu ka ga wane ladani za ka yi
aiki da kiransa, domin akwai dubban matsaloli a wannan bangaren, wani ladanin
fa sai wani masallacin ya fara sallah sannan shi zai kira, tirkashi!.
BUDA BAKI.
Shi ne abinda mai azumi yake ci ko sha
bayan faduwar rana. Ke nan abinda ake so anan shi ne da zarar rana ta fadi
kawai sa ka sha ruwa, wannan shi ne karantarwa musulunci domin rana na faduwa
an shiga farkon dare, kuma Allah madaukakin sarki cewa ya yi:
((وكلوا واشربوا حتى
يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر، ثم أتموا الصيام إلى اليل)).
البقرة
Ma’ana: Kuma ku ci ku sha, har sai silin farin
zare ya bayyana daga silin bakin zare na alfijr, sannan kuma ku cika azuminku
zuwa dare.” Bakarah.
Anan Allah madaukakin sarki ya yi bayanin
farkon azumin da kuma karshensa, farkonsa shi ne fitowar alfijir, karshen sa
kuma faduwar rana.
Sannan a karantarwar musulunci suhur
jinkirta shi ake yi, wato ba’a yin shi a farkon dare ko tsakiyar dare, kamar
yadda bayani ya gabata. Shi kuma buda baki gaggauta shi ake yi, wato da zarar
rana ta fadi.
Ba birgewa ba ce mutum ya ce ai shi sai
an yi sallar magariba yake shan ruwa, a’a abinda ake so shi ne da zarar lokacin
shan ruwa ya yi ka sami wani abu ko kadan ne ka sa a bakinka. An fi so ya zama
dabino in ba’a samuba sai ruwa.
BUDA BAKI A LOKACIN DAMINA.
Ya zama dole a dunga lura musamman lokacin
damina, domin idan gari ya rufe da hadari, domin wasu ladanan kawai sai su
danno kiran sallah da kusan banbancin minti goma ko talatin wani lokacin ma awa
daya akan yadda suka kira jiya. Saboda haka dole ka tsaya ka natsu domin sanin
wanne ladani za ka bi a bude baki da kuma suhur.
BUDA BAKI A JIRGIN SAMA.
Akan abinda ya shafi buda baki a cikin
jirgin sama to bayanan za su kasance ne kamar haka:
(1) Idan kuka ta shi daga filin jirgin
sama sai kawai kuka dare to shikenan lokacin san ruwanku ya yi, ba za ka yi
la’akari da inda kuka taso ba cewar ai ba’a sha ruwa ba, tunda dai yanzu inda
kuke rana ta fadi shikenan sai ku sha ruwa.
(2). Idan said a kuka sha ruwa, sannan
sai kuma jiginku ya tashi, jirgin yana tashi sai kuma ga rana a sama, to anan
malamai suka ce za ku ci gaba da cin abincin ku ne kawai babu wata matsala,
domin tun farko kun ajiye azuminku a bisa ka’ida ta shari’a.
(3) Idan ya zama rana ba ta fadi ba kuka
tashi, sai ya zama kuma ga ranar nan kuna gani, to anan fa babu yadda za’a yi a
yi buda baki sai rana ta fadi, ba za ku yi la’akari da kasar da kuka baroba ko
kuma kasar da za ku je, cewar an sha ruwa a can ko ba’a sha ba, duk ba za’a
la’akari da wannan ba, kawai hukuncinku shi ne hukuncin nan wurin da kuke. Ka’ida
fa a babin azumi dauka ko ajiyewa shan ruwa ko suhur shi ne hukuncin nan inda
kake, sauda yawa zai zama kuma tafiya kuna bin rana, to shakka babu tsawon
lokacin buda bakinku zai karu, ko kuma kun juwa rana baya to kuma tsawon
lokacinku na shan ruwa zai ragu.
TSAWON LOKACI KO GAJARTARSA A BUDA BAKI.
Idan kasar da kake rana na fitowa kuma ta
fadi, to anan sahur dinka da buda bakinka ya ginune akan fitowar alfijir a
daina sahur, fadur rana kuma a yi buda baki, sabo da fadin Allah madaukakin
sarki:
((وكلوا واشربوا حتى
يتبين لكم الخيط الأبيض من الخيط الأسود من الفجر، ثم أتموا الصيام إلى اليل)).
البقرة
Ma’ana: Kuma ku ci ku sha, har sai silin farin
zare ya bayyana daga silin bakin zare na alfijr, sannan kuma ku cika azuminku
zuwa dare.” Bakarah.
Idan misali inda kake rana tana fitowa ne
tsawon awa biyar sannan ta fadi, sannan kuma dare ya zo awa shatara, to haka za
ku yi azuminku cikin wadannan awannin, ta yadda da rana ta fadi shikenan sai ku
yi buda baki.
Haka kuma idan inda kuke rana ce take
fitowa tsawon awa shatara misali ko ma sama da haka to fa ba makawa a wadannan
awannin zaka yi azumi, koda a ce awa ashirin da biyu ne arana, awa biyu kuma
dare, to awadannan awannin ashirin da biyu a shi ne za ku yi zumi, suma sauran
awa biyun a su ne za ku yi buda baki da magariba da isha da tarawih da kuma
sahur, saboda waccan ayar da aka anbata a sama. Wannan yana nuna mana cewar ya
zama dole mu tashi mu koyi sanin hukunce hukuncen ayyukammu na addinin
musulunci ta yadda duk inda ka sami kanka to kasan hukuncin day a kamaka, domin
kada mutum ya dauki hukuncin kasarsa ya ce da shi zai yi aki a ko’ina.
Kammalawa: Da wannan ne muka karshen wannan bayani
akan abinda ya shafi sahur da kuma bude baki, da kuma abubuwan da suke da alaka
da su.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com