Gabatarwa: A wannan karon zamu
kawo bayanaine akan abinda ya shafi yin kabaliyyah ko ba’adiyyah a salloli na
nafila.
Shinfida: Da farko mu sani
cewar duk abinda yake farillane a sallah kuma akabarshi to kabaliyyah ko
ba’adiyyah bata gyarashi, to haka hukuncin yake a salloli na nafila?. Haka kuma
duk abinda mustahabbine a sallah to shima ba’a yi masa kabaliyyah ko
ba’adiyyah.
Dukkan rafkannuwa
da aka yi ta a lokacin da ake ramuwar sallah to hukuncinta kamar sallar da ake
yenta ne a cikin lokaci, kenan ba banbanci da sallolin ramuwa da kuma wadanda
ake yinsu cikin lokaci.
Yin rafkannuwa a
sallar nafila hukuncinsa kamar yin ranfannuwa ne a sallolin farilla in banda
mas’aloli guda shida ananne nafila ta banbanta da farilla, sune kuma kamar
haka:
(1) Karatun Fatiha: Duk
wanda ya manta da karatun fatiha a sallar nafila bai tunaba sai bayan ya yi
ruku’u sannan ya tuna to anan zai ci gaba da sallar shine sai bayan ya kammala
ya yi kabaliyyah, sabanin sallar farilla da zai cire wannan raka’ar ya kawo
wata makwafinta sannan ya yi ba’adiyyah idan ba’a biyun farko bane, ko
kabaliyyah idan hakan ya farune a biyun farko na farilla.
(2) Karatun Sura.
(3) Bayyanawa.
(4) Sirrantawa.
Idan mutum ya
manta karatun sura bayan fatiha a cikin sallar nafila, ko kuma ya bayyana a
inda ake asurtawa ko ya sirranta a inda ake bayyanawa kuma bai tunaba sai bayan
da ya yi ruku’i to zai ci gaba da sallar shine, amma duka a cikin nafila to
babu komai akansa, wato ba kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, sabanin inda sallar
farilla ce.
(5) Tashi Zuwa Raka’a Ta Uku: Dun
wanda ya kammala raka’o’I biyu a sallar na fila sai bai zaunaba ya mike zuwa
raka’a ta uku to idan ya tuna kafin ya kulla ruku’u to anan zai dawo ya zauna
ya yi tahiya ya yi sallama, sannan kuma ya yi ba’adiyyah, amma har idan ya
kulla raka’a ta uku to zai ci gabane da sallar sai ya karat a zama raka’o’I
hudu sannan sai ya yi kabaliyyah, sabanin sallar farilla.
(6) Manta Rukuni: Duk
wanda ya manta rukuni a sallar nafila kamar ruku’i ko sujjada kuma bai tuna ba
har ya yi sallama kuma abin ma ya yi tsawo to anan ba zai sake sallar ba,
sabanin sallar farilla, domin inda farillace to da zai sake sallarne har abada.
Kammalawa: Wadannan sune
wuraren da aka dan sami banbanci tsakanin salloli na farilla da salloli na
nafila akan abinda ya shafi hukunce-hukuncen rafkannuwa, da fatan Allah ya
anfanar da mu.
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna Jahar Neja,
Nijeriya.
Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com