Wednesday, March 13, 2013

Abubuwa Bakwai Masu Halakarwa(Cin Dukiyar Maraya)5/7#


Cin Dukiyar Maraya: A yanzu za mu yi bayani akan abu na biyar cikin abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine Cin Dukiyar Maraya.
Maraya: shine wanda mahaifinshi ya rasu kafin ya balaga ya yi hankali. Ma'aikin Allah ya ja kunnen al'umma sosai da sosai akan kulawa da hakkin maraya da tausaya masa, da fadi-tashi akan al'amuransa kuma ya bayyana falalar hakan awurare dadama. To amma abin takaici sai awayi-gari dan abinda uba ya mutu ya barwa 'ya'yansa sai wani/wasu subi takan wannan abinda aka bari kafin dan lokaci ane meshi a rasa. Allah madaukakin sarki yana cewa dangane da masu cin dukiyoyin marayu da zalunci: ''Lalle dukkanin wadanda suke cin dukiyoyin marayu da zalunci, abin sani kawai suna cin wutane a cikinsu, kuma da sannu za'a kona su a wuta wacce ake rurata'' Suratun Nisa'I, aya ta:10.
       Akwai hanyoyi da dama da mutane suke bi wurin cinye wannan dukiya ta maraya, wasu idan suna hurda da mutum sai ya zama akwai wasu kudadensa ko filayansa komadai wasu kadarori da yasan ba wanda ya sani sai shi, sai kawai ya yi shiru akansu ya ki fito da su in kuma ya ga suna da yawa ko za'a gane sai ya dan tsakuro wasu daga ciki sauran kuma ya yi shiru akansu, ana samun masu irin wannan mummunan hali cikin matan mamacin ko 'ya'yanshi ko abokanshi ko abokan cinikayyarsa d.s, wannan haramunne ko tantama babu kuma duk wanda ya yi irin wannan hali sai ya amayar da abinda ya ci a ranar alkima alokacin da hakan ba zai yi anfaniba.
      A wasu wuraren kuwa hukumomin yankinne –masu unguwanni da dagatai Hakimai (wadanda ake kira masu kasa) suke wadaka da abinda akabarwa magada said an abinda aka sammusu, gonakine ko fadamu ko madaime aka bari.
       A wani lokacin kuma shi malamin da kakira domin ya raba gado shine wanda zai kamfaci wani kaso mai tsoka yace wannan na masu rabone, ko kuma a zaga ta baya ahada baki dashi don ya karawa wani, waifa wanda zai yi fada akan wannan mummunan hali shine kuma zai zama ja-gaba, Allah ya sawwake.
       Awani jikon kuma 'ya'ya mata da matan mamacin sune za'ayi rabon gado amma kwatata-kwata basusan me aka rababa, ko dai 'yan-uwan mamacin su yi watsi da su ko kuma 'ya'ya maza su yi watsi da 'yan-uwansu 'ya'ya mata, ko kuma duk ba wannan ba wacce tafi 'ya'ya sai tai zamanta akan dukiyar kaji don rashin jin tsoron Allah wai ana cewa ba'a raba gado da mara 'ya'ya, sauda yawa wata irin kazantar da ake yi awurin rabon gado kare ba zai ci ba.
       Awani karon kuma shi wanda akaba dukiyar marayun ya kula da ita bayan an gama rabo shine zai hauta da casa kafin-kiftawa-da bisimillah ya hallaka dukiyar bakidayanta.
       Bai halatta a dankawa yara kanana dukirasu ta gadoba sai bayan sun cika sharudda guda biyu:
(1) Balaga: Dole kai da akaba dukiyar mamaci ka ci gaba da riketa kana jujjuyata ba zaka danka masaba sai ya balaga, ita kuma alamar mutum ya balaga alamace kamar haka:
(a) Mafarki: Alokacin day a yaro ko yarinya ta yi ko ya yi mafarkin ya sadu da mace ko macen an sadu da ita kuma mani ya fita, to daga wannan lokacin hukunce-hkuncen shara'a sun haukanshi ko kanta mala'iku za su dinga rubuta musu ayyukan da kowa ya yi mekyau ko mara kyau sun yi aure ko ba su yi aureba domin babu wanda yace sai mutum ya yi aure sannan za'a bude masa fayil a wurin Allah. Ko kuma maniyyin ya fita a farke ba wai sai abacciba kadai.
(b) Bayyanar Gashin Mara: Hakanan idan gashin mara mai kaush-kaushi ya bayyana a gaban 'Ya mace ko Da namiji.
(C) Jinin Al'ada: Hakanan daga lokacin da mace ta ga jinin al'ada to daga wannan lokaci ta balaga hukunce-hukuncen Allah sun hau kanta, anan nake cewa dolene iyaye su tashi tsaye wurin kula da 'ya'yansu.
(d) Cika shekara 15: Alokacin da Dan amiji ya cika shekara 15 ko 17 ko 18, kamar yadda malamai suka karawa juna sani to lalle ya balaga.
  Wadannan alamun balaga ko wacce daya cingashin kanta take yi, ba lalle bane cewa sai sun bayyana duka, alokacin da daya ta bayyana shekenan, kuma ya zama dole iyaye da masu ruko su kula sosai da sosai, domin sai kaga yaro ko yarinya sun sha azumi amma kwatakwata ba maganr ramawa wai andauka sai anyi aure sannan mutum zai dinga cika ibadarsa.
(2) Sharadi Na Biyu Wayau: Koda yaron da kake kulawa da dukiya  ya balaga to bai halatta ka bashi dukiyarba sai ka jarraba hankalinsa da dabararsa da wayonsa, idan ya natsu sai ka danka masa, idan kuwa bai natsuba to bai halatta ka bashiba.
Wadannan sharudda guda biyu sune aya ta: 6 cikin Suratun Nisa'I ta yi bayani, Allah madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma ku jarraba marayu har idan suka isa aure to idan kun tabbatar da wayonsu sai ku ba su dukiyoyinsu, kada ku ci ita (dukiyar) da barna da gaggawa kafin su girma (komai yak are), duk wanda yake mawadacine to ya kame, wandako fakirine (marashine) to ya ci gwargwadon wahalarsa, idan zaku danka musu (dukiyar) to ku kafa musu sahaida, lalle Allah Ya isa mai lissafi akan komai''.
Wannan babbar ayace akan abinda ya shafi kulawa da dukiyar maraya a tsari mai cike da adalci da tausawa da baima kowa hakkinsa. Da farkodai ayar ta yi nuni da adinga jarraba su marayun har idan aka ga sun cika wadancan sharudda biyu sai aba su dukiyarsu, sannan ayar ta ja kunnen masu kula da dukiyar da kada su tasata a gaba da ci ham-ham kafin yara su girma babu komai, sai ayar ta bayya hakkin mai kula da dukiyar idan shi mai kula da dukiyar maraya dama mawadacine yana da harkokinshi to ya ci gaba da kulawa da amma ya kame daga cin wani abu na dukiyar, idan ko talaka kulawa da dukiyar marayan ta shagaltar da shi daga nashi fadi-ta-shin, to ya dauki gwargwadon wahalarsa, ma'ana inda wani kadauka aiki yake kulama da dukiyarka nawa zaka bashi, to abinda kasan zaka bashi haka zaka dauka.
     Sannan ayar ta nuna mana cewa idan lokacin dankawa maraya dukiyarsa ya yi kada ku kunshe kanku a daki a'a ku kafa shaidu, to kenamma a lokacin da zaka karbi dukiyar maraya ka tabbatar ansa shaidu kuma a rubuta adadin abinda ka rike, kada ka yarda ace ai ba sai anrubutaba ba danka bane, sauda yawa mutum ba zai raka kaba yace dare ya yi ma, wasu su za su zugo maryun bayan sun girma ace babanku yabar muku abukaza da abu kaza a nemi a hada ka fada da 'ya'yan kaninka ko yayanka, Allah Ya sawwake, sannan wurin shaidun ba lalle bane ace sai dattijai a hada da matasa wada suke da wayau Allah ne dai kadai yasan gawar fari.
Sai Allah Ya rufe ayar da ya isa ya zama mai lissafi, wannan yana nuna mana cewa a tsaya ayi lissafi mai kyau lokacin karba da kuma lokacin bayarwa, zaka lissafa duk abinda kake kashewa marayan dake hannunka kamar kudin makaranta, kudin koyon sana'a, domin zaka tsayane ka kula da tarbiyyarsa lokacin muzurai ayi mishi muzurai, lokacin fada ayi mishi fada in ya yi abin duka adoke shi amma ba duka mai tsananiba, domin sai an rintse ido akeshan magani musamman a rirn wannan lokaci ta tarbiyya ta sukurkuce. Kasa shi makarantar Islamiyyah data book da koyon sana'a, sai kaga ya girma ya zama natsattsen mutum kamili, ga kuma irin wannan dinbin lada da kasamu, domin duk wadannan al'amurra da kake wa wannan maraya kana da lada na musamman awurin Allah.
Ayoyin Alkur'ani mai girma sun zo da bayanin kada ku yi kusa da dukiyar maraya said a abinda yake shine mafi kyau, saboda yadda ayoyi suke Magana akan dukiyar maraya saida yakai wasu sun nemi su ware dukiyarsu data maraya ba tare da sun hadaba koda ko jinsinsu guda kamar dabbobi kayan gona kudi d.s, a Suratul Bakara aya ta: 220, Allah madaukakin sarki yana cewa:
''Kuma suna tambayarka dankane da marayu, kace: Kyautata musu shine daidai, har idan kuka hada (dukiyarku da ta su ai 'yan-uwankune (ba komai), Allah Yasan mabarnaci kuma ya san mai gyara''.
Kuma ya kamata al'umma su tsaya su yi karatun-ta natsu akan marayu bai gagara mutum shima ya mutu ya bar na shi yaran kanana  ai shima ba zai so abinda ya bar musu wani ya yi wadaka da shiba.
Saboda haka lissafa cin dukiyar maraya ba-gaira-ba sabab da Ma'aikin Allah ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa ba karamin tashin hankali bane
Kammalawa: Awannan takaitaccan bayani day a gabata lalle munsan irin hakkin da maraya yake da shi, da kuma wajibcin tsayawa tsayin-daka akan akula da dukiyar maraya, sannan da bayanin minzalin da maraya zai kai sannan a danka masa dukiyarsa, sannan da bayanin cewa wannan aiki ba karamin matsayi yake da shi a wurin Allah ba, wannan kuma zai dada fayyace mana yadda musulunci a kullum yake kulawa da masu rauni, sannan ga shi yadda bayani ya gabata wadanda suka fi shan wahala sune mata da kananan yara, kuma ga yadda Allah Ya yi bayani akan dukkan mai cin dukiyar maraya da zalinci to wuta yake cima cikinsa, Allah Ya tsaremu kuma dukkan wadanda suke kula da marayun dake hannunsu ya Allah ka taimaka musu wurin sauke wannan nauyi, kuma Ya Allah ladan da kake baiwa wadanda suke kulawa da marayu ya Allah ka tabbatar mana mu da su baki daya, Amin.
Aliyu Muhammad Sadisu,
 Kwakungu, bayan Ofishin 'Yansanda.
 Minna, jahar  Neja Nijeriya.
 Za'a iya tuntuba a (+234)08064022965,
ko kuma a: e-mail:aliyusadis@gmail.com
Ko a ziyarcemu a yanar gizo, a :
htt:// munbarin-musulunci.blogspot.com
: munbarin musulunci

No comments:

Post a Comment